Shugaba Bola Tinubu Ya Sa Labule da Goodluck Jonathan bayan Sukar 'Yan Adawa

Shugaba Bola Tinubu Ya Sa Labule da Goodluck Jonathan bayan Sukar 'Yan Adawa

  • Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ziyarfi fadar Aso Rock Villa da ke Abuja domin ganawa da Shugaba Bola Tinubu
  • Goodluck Jonathan ya kai ziyara fadar shugaban kasar ne da yammacin ranar Laraba, 22 ga watan Afirilun shekarar 2026
  • Ganawar dai na zuwa ne bayan Goodluck Jonathan ya kai irin wannan ziyarar a watan Nuwamban shekarar da ta gabata

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Abuja, tarayyar Najeriya - Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya kai ziyara ga Shugaba Bola Tinubu.

Goodluck Jonathan ya kai ziyara ga Shugaba Tinubu ne a fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock da ke Abuja a ranar Laraba, 22 ga watan Afirilun 2026.

Jonathan ya ziyarci Shugaba Bola Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu tare da Goodluck Jonathan a fadar Aso Rock Villa Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Ziyarar wadda aka yi ta kusan ƙarfe 4:00 na yamma, an tabbatar da ita ne ta hannun mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Kotu ta dauki matakin farko kan wadanda ake zargi da yunkurin yi wa Tinubu juyin mulki

Goodluck Jonathan ya gana da Bola Tinubu

Bayo Onanuga ya wallafa hotunan taron inda ya rubuta cewa:

“Shugaba Tinubu ya gana da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a fadar shugaban kasa.”

Hotunan sun nuna dukkan mutanen biyu suna gudanar da tattaunawa cikin natsuwa, tare da wata takarda mai taken “Two-Year Milestone” da ake iya gani a kusurwar ofishin shugaban kasar.

Ganawar ta ranar Laraba na daga cikin jerin tattaunawa da shugabannin biyu ke yi akai-akai kan al'amuran siyasar Afirka ta Yamma da kuma ayyukan Najeriya a nahiyar Afirka.

Jonathan ya ziyaci Tinubu a baya

Babu wata sanarwa a hukumance da aka fitar game da abubuwan da aka tattauna, amma ganawar ta ranar Laraba ta zo ne watanni bayan ziyarar ƙarshe da Jonathan ya kai a watan Nuwamban 2025.

Jonathan ya ziyarci fadar ne a ranar 29 ga Nuwamba, 2025, sa’o’i kaɗan bayan an dauko shi daga birnin Bissau biyo bayan juyin mulkin da sojoji masu biyayya ga Birgediya-Janar Dinis Incanha suka yi.

Kara karanta wannan

Kurunkus: An gurfanar da mutane 6 da ake zargi da yunkurin yi wa Tinubu juyin mulki a Najeriya

Sojojin sun kama shugaba mai ci Umaro Sissoco Embaló ranar 26 ga Nuwamba, kwana ɗaya kafin hukumar zaɓe ta sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na ranar 23 ga Nuwamban 2025 a hukumance, jaridar The Punch ta kawo rahoton.

A wancan lokacin, Jonathan ya jagoranci tawagar sanya ido kan zaɓe ta kungiyar dattawan Afirka ta Yamma, kuma an dauke shi ne a cikin wani jirgi mai saukar ungulu.

Shugaba Tinubu ya karbi bakuncin Goodluck Jonathan
Shugaba Bola Tinubu na gaisawa da Goodluck Jonathan yayin ziyarar da ya kawo masa Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Jonathan ya yi kira ga shugabannin ECOWAS

A wancan taron na watan Nuwamba, tsohon shugaban ya yi kira ga shugabannin ECOWAS da su tabbatar da sakin ɗan takarar adawa Fernando Dias da Costa da kuma sanar da sakamakon zaɓen.

Jonathan ya shafe mafi yawancin shekaru 10 da suka gabata yana aiki a matsayin mai sanya ido kan zaɓe kuma mai shiga tsakani a Afirka ta Yamma.

Ya gudanar da ayyuka a Mali, Gambia, Liberia da kuma Guinea-Bissau a ƙarƙashin inuwar kungiyar dattawan Afirka ta Yamma.

Shugaba Tinubu ya soki 'yan adawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kakkausar suka ga 'yan adawa.

Shugaba Bola Tinubu wanda ya hau kan karagar mulki tun shekarar 2023 ya 'yan adawa da raunana dabi’un dimokuradiyya yayin da suke ikirarin kare su.

Mai girma Bola Tinubu ya jaddada cewa dimokuradiyya za ta dore a Najeriya duk da abin da ya kira tsoratarwar da ake yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng