Da Gaske Gwamnan APC zai Ajiye Mulki saboda Rashin Lafiya? Gaskiya Ta Fito
- Tun jiya aka fara yada jita-jitar cewa gwamna Babajide Sanwo-Olu na fama da rashin lafiya kuma zai ajiye mulki ya mika ga mataimakinsa
- Hakan na zuwa ne 'yan sa'o'i bayan Babajide Sanwo-Olu ya amince da mataimakinsa zai yi takara a zaben 2027 domin ya gaje shi
- Sai dai gwamnatin Legas ta yi karin bayani game da halin da gwamna Sanwo-Olu ke ciki game da lafiya da kuma batun mika mulki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos - Gwamnatin Jihar Legas ta yi watsi da rahotannin da ke cewa an bukaci Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya yi murabus saboda dalilan rashin lafiya, tana mai bayyana labarin a matsayin karya.
Gwamnatin ta soki wani rahoto da wata kafar yanar gizo ta wallafa, tana mai jaddada cewa babu wani tushe na gaskiya a cikinsa.

Kara karanta wannan
Gwamnan Legas ya bi sahu, ya nuna wanda yake goyon bayan ya gaje shi a zaben 2027

Source: Facebook
Da gaske Babajide Sanwo-Olu zai yi murabus?
Puch ta wallafa cewa mai ba gwamna Sanwo-Olu shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Gboyega Akosile, ya ce maganar rashin lafiyar ba ta da tushe.
Sanarwar ta ce:
“Mun lura cewa hankula sun tashi kan labarin karya da aka yada, wanda ke cewa an ‘tilasta wa Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya yi murabus saboda rashin lafiya’ tare da cewa mataimakin gwamna zai karbi ragamar mulki.
“Wannan rahoto karya ne gaba daya. Babu wanda ya bukaci gwamnan Legas ya sauka daga mukaminsa. Wannan wata sabuwar jita-jita ce ta karya da ta zama ruwan dare.
“Gwamna Sanwo-Olu na cikin koshin lafiya, hankalinsa a kwance yake, kuma yana ci gaba da gudanar da ayyukansa na shugabanci yadda ya kamata.”
Gwamna Sanwo-Olu ya gana da mataimakinsa
Gwamnatin ta kuma yi karin bayani kan rahotannin wata ganawar siyasa tsakanin gwamnan da mataimakinsa, inda ta ce:
“A yau da safe, gwamnan ya karbi bakuncin mataimakin gwamna, Dr Kadri Obafemi Hamzat, wanda ya kai masa ziyara domin sanar da shi niyyarsa ta tsayawa takarar gwamna.
"An gudanar da ganawar cikin mutunci da fahimtar juna, kamar yadda aka saba.”

Source: Facebook
Kiran gwamnatin Legas ga jama'a
Rahoton PM Nigeria ya nuna cewa gwamnatin Jihar Legas ta bukaci jama’a da su yi watsi da wannan rahoto, tana mai jaddada cewa labarin karya ne kawai.
Ta kuma tabbatar da cewa Gwamna Sanwo-Olu na ci gaba da tafiyar da harkokin jihar ba tare da wata tangarda ba, yana kuma sauke nauyin da ya rataya a wuyansa yadda ya kamata.
APC ta samu 'dan takarar gwamnan Legas
A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya amince da takarar mataimakinsa, Dr Kadri Obafemi Hamzat.
Gwaman bayyana haka ne a ranar Litinin, 27 ga watan Afrilun 2026 yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC da aka gudanar.
Babajide-Sanwo Olu ya yi fatan samun nasara ga mataimakinsa a zaben 2027 tare da sauran wadanda za su yi takara karkashin jam'iyyar APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
