2027: Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai da Sanatan Abia Sun Tada Rigima a Jam'iyyar APC

2027: Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai da Sanatan Abia Sun Tada Rigima a Jam'iyyar APC

  • Jam'iyyar APC reshen jihar Abia ta tsinci kanta a rikicin shugabanci tsakanin Sanata Orji Kalu da Rt. Hon. Benjamin Kalu
  • Sanatan da kuma mataimakin shugaban Majalisar wakilai ta kasa sun yi ikirarin cewa Bola Tinubu ya wakilta su don su jagoranci APC a Abia
  • Wannan lamari na neman raba kan APC a jihar yayin da ake shirye-shiryen tunkarar babban zaben 2027 mai zuwa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abia - Rikici ya barke tsakanin Sanata Orji Uzor Kalu da mataimakin shugaban Majalisar Wakilai ta tarayya, Rt. Hon. Benjamin Kalu kan jagorancin APC a jihar Abia.

Sanata Kalu, wanda tsohon gwamnan Abia ne ya yi ikirarin cewa shi ne jagoran APC a Abia, haka a bangaren Benjamin Kalu, ya ce shi aka nada ya jagoranci harkokin APC.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Ganduje ya amsa kiran masoya Tinubu, zai nemi kujerar sanata a Kano

Kalu.
Mataimakin shugaban majalisar wakilai ta kasa, Rt. Hon. Benjamin Kalu a zauren Majalisa a Abuja Hoto: @HouseNGR
Source: Twitter

Premium Times ta ruwaito cewa dukkannin ‘yan siyasar biyu sun ce Shugaba Bola Tinubu ne ya ba su umarnin jagorantar harkokin jam’iyyar APC a jihar Abia.

Orji Kalu, wanda ke wakiltar Abia ta Arewa a Majalisar Dattawa, ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a Facebook, inda ya gode wa shugaban kasa kan amincewa da shi.

Ya ce zai hada kai da dukkan masu ruwa da tsaki domin tabbatar da APC ta tsayar da ‘yan takara masu farin jini a wurin jama'a domin samun nasara a zaben 2027

Benjamin Kalu ya mayar da martani

A nasa bangaren, Benjamin Kalu ya karyata ikirarin Sanatan, yana mai cewa shugaban kasa ya fi karkata ga tsarin da ke bai wa manyan masu rike da mukamai irin nasa damar tafiyar da harkokin APC.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Benjamin ya ce wannan tsari ne da aka dade ana amfani da shi wanda ya taimaka wajen hada kan jam’iyya da kuma samun nasarori.

Kara karanta wannan

Rurum ya samu goyon baya domin maye gurbin Kawu Sumaila a Majalisar Dattawa

Abin da ya haddasa wa APC rikici a Abia

Rahotanni sun nuna cewa wannan takaddama na da nasaba da zaben gwamnan jihar Abia na shekarar 2027.

Benjamin Kalu na da burin tsayawa takarar gwamna a karkashin APC, haka kuma, kaninSanata Orji Kalu, Mascot Kalu, shi ma ya nuna sha’awar neman tikitin jam’iyyar domin takarar gwamna.

Benjamin Kalu.
Mataimakin kakakin Majalisar wakilai, Benjamin Kalu lokacin da ya ziyarci Shugaba Bola Tinubu da Sanata Orji Uzo Kalu Hoto: Senator Orji Uzor Kalu
Source: Facebook

Fargabar rabuwar kai a jam'iyyar APC

Wani jigo a APC a jihar, Agwu Emeaba, ya yi gargadi cewa rikicin na iya janyo rabuwar kai a jam’iyyar musamman kan goyon bayan da wasu suka bai wa Benjamin Kalu

A nasa bangaren, Mascot Kalu ya ki amincewa da wannan goyon baya da aka nuna wa mataimakin kakakin majalisar.

Sanatan PDP ya koma APC a Gombe

A wani labarin, kun ji cewa sanata mai wakiltar mazaɓar Gombe ta Kudu a Majalisar dattawa, Anthony Siyako Yaro, ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki.

Mai magana da yawun gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jjhar Gombe, Ismaila Uba Misilli, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Legas ya bi sahu, ya nuna wanda yake goyon bayan ya gaje shi a zaben 2027

Sauya shekar sanatan ta sanya jam'iyyar APC ta kara karfafa karfin da take da shi a jihar Gombe yayin da ake tunkarar babban zaben shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262