Sale Mamman: Abin da yasa ban koma gidana ba tun bayan da Buhari ya kore ni

Sale Mamman: Abin da yasa ban koma gidana ba tun bayan da Buhari ya kore ni

  • Tsohon ministan makamashi, Sale Mamman, ya karyata rahoton cewa ya suma an kuma kwantar da shi a asibiti bayan labarin korarsa
  • Mamman ya bayyana cewa tun karshen makon da ta gabata dama ba shi da lafiya kuma yana zuwa asibiti amma ba a kwantar da shi ba kuma bai suma ba
  • Tsohon ministan ya kuma ce likitansa ya umurci ya huta shi yasa bai koma gidansa ba ya samu wani wuri ya fake don kada masu jaje su hana shi hutawa

Sale Mamman, tsohon ministan makamashi, ya yi bayanin abin da yasa bai koma gidansa ba bayan shugaba Muhammadu Buhari ya sallame shi daga aiki, rahoton Daily Trust.

Wasu rahotanni sun ce an kwantar da ministan a asibiti bayan ya samu labarin cewa an kore shi.

Kara karanta wannan

Saleh Mamman ya yi magana a Facebook, awa 24 bayan Buhari ya tunbuke shi daga Minista

Ban suma ba, ba a kwantar da ni a asibiti ba: Ministan da Buhari ya kora ya faɗi abinda yasa bai koma gida ba
Tsohon Ministan Makamashi, Sale Mamman. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Amma, a wata hirar wayar tarho da ya yi da BBC Hausa, Mamman ya karyata rahoton.

Ko mene yasa Sale Mamman bai koma gidansa ba bayan an kore shi?

Tsohon ministan ya amsa cewa tabbas ba shi da lafiya, amma ya ce tun makon da ta gabata ya ke shan magunguna saboda rashin lafiyan.

Ya ce:

"Tun kafin a sanar cewa an kore ni, ina fama da rashin lafiya. Ban tafi ofis ba tun farkon wannan makon."
"Jiya (Laraba) da yau (Alhamis) na sake komawa asibitin saboda a sake duba ni; kuma likitan ya bada umurnin cewa ina bukatar hutu don haka na tsaya a wuri daya domin in huta.
"Na samu wani wuri mara hayaniya domin in huta in kuma sha magungunan da likitan ya bani. Ban zauna a gida na ba domin masu zuwa jaje suna ta zuwa; hakan zai hana ni samun hutu a yanzu.

Kara karanta wannan

Shekaru 35 yana aikin koyarwa a Borno, dan Najeriyan da Turawa suka horar ya koma talla

"Amma ba a kwantar da ni a asibiti ba, kuma ban suma ba kamar yadda aka ruwaito."

A waya Buhari ya sanar da ni cewa an kore ni, Sale Mamman

Mamman ya kuma ce a daren ranar Litinin, Buhari ya kira shi a waya domin sanar da shi cewa za a sallame shi.

Ya ce:

"Ko an kore ni, ko ba a kore ni ba dama zan sauka nan da shekaru biyu."

An nada Mamman ne a matsayin minista a ranar 21 ga watan Agustan 2019.

An sallame shi ne tare da Sabo Nanono, tsohon ministan noma a ranar 1 ga watan Satumban 2021.

Buhari ya bayyana dalilin da ya sa ya kori ministocinsa biyu

Tunda farko, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da yasa ya sallami ministoci biyu daga cikin yan fadarsa da ya zaba a ranar 21 ga watan Agustan 2019.

Sanarwar da kakakin shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar ta ce bukatar 'sabon jini' ne yasa aka yi sauyin ministocin kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi: Kotu ta soke dakatarwar da aka yi min a matsayin Shugaban APC, Oshiomhole ya bayyana mataki na gaba

An maye gurbin su da Dr Mohammed Mahmood Abubakar, Ministan Muhalali da Abubakar D. Aliyu, Karamin Ministan Ayyuka da Gidaje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel