Manyan 'Yan Siyasar Adawa da Suka Je Kano domin Karbar Kwankwaso cikin ADC
- Tsohon ɗan takarar Shugaban ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fice daga NNPP, ya koma jam’iyyar ADC a hukumance
- An ba shi katin zama ɗan jam’iyya a Kano, a Gidan Kwankwasiyya a ranar Litinin, 30 ga watan Maris na shekarar 2026
- Legit ta tattaro fitattun ‘yan siyasa da dama da suka hallara a gidansa domin halartar bikin sauya shekar a jiya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano –Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, zama cikakken ɗan ADC a hukumance.
Kwankwaso, wanda ya taɓa rike mukamin ministan tsaro a Najeriya, ya kammala rajista a sabuwar jam’iyyarsa inda aka karɓe shi tare da ba shi katin zama ɗan jam’iyya.

Source: Facebook
Channels TV ta wallafa cewa an gudanar da wannan muhimmin taro ne a Gidan Kwankwasiyya da ke Miller Road a unguwar Bompai, Kano. Matakin na Kwankwaso na zuwa ne a wani lokaci da ake samun sauye-sauyen siyasa a ƙasar, musamman ta fuskar sauya sheka da karban sabuwar shahadar siyasa.
Dalilin da ya sa Kwankwaso ya bar NNPP
Jaridar Punch ta ruwaito cewa akwai rikice-rikice da rashin jituwa a cikin NNPP, wanda hakan ya iya taka rawa wajen yanke shawarar ficewar tasa.
Ana ganin cewa komawar Kwankwaso zuwa ADC na iya sauya fasalin siyasar Najeriya, musamman a yankin Arewa, inda yake da tasiri mai ƙarfi.

Source: Facebook
A yayin wannan sauya sheƙa, an ga ko aka ambaci fitattun ‘yan siyasa da dama da ake alaƙanta su da wannan sabon tafiyar.
Daga cikinsu akwai tsofaffin Ministoci da gwamnoni, yayin da ake da wadanda ke rike da zabbiyar kujera a yanzu.
Wasu wadanda suka karbi Kwankwaso zuwa ADC
Rohoton nan ya tattaro jerin manyan 'yan siyasar da aka gani a gidan Kwankwaso.
Daga cikinsu akwai shugabannin jam'iyyar ADC na kasa baki daya, Sanata David Mark da kuma sakatarensa Rauf Aregbesola.
Haka zalika an ga Peter Obi wanda ya yi wa LP takara a zaben 2023, wasu sun fara rade-radin hada shi a tikiti tare da Rabiu Kwankwaso.

Kara karanta wannan
NNPP ta gaza hakura da jagoranta, za ta yi haɗaka da ADC bayan Kwankwaso ya sauya sheka
1. Sanata David Mark
Sanata David Mark tsohon soja ne kuma gogaggen ɗan siyasa, wanda ya rike muƙamin Shugaban Majalisar Dattawa daga 2007 zuwa 2015 a ƙarƙashin PDP.
Ya kasance ɗaya daga cikin manyan masu daidaita harkokin jam’iyyar, amma daga baya ya fara nuna rashin gamsuwa da rikice-rikicen cikin gida da raguwar tasirinsa.
A yanzu shi ne Shugaban jam'iyyar ADC na ƙasa da ke jagorantar ƴan adawa wajen shirin kwace mulki daga APC.
2. Peter Obi
Peter Obi tsohon gwamnan jihar Anambra ne kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LPa 2023, inda ya samu gagarumin goyon bayan matasa.
A baya ya kasance jigo a PDP kuma ya taba zama abokin takarar Atiku Abubakar, inda ya nemi mataimakin shugaban ƙasa a 2019.
Yana daga cikin jiga-jigan ADC waɗanda aka sake fasalta jam'iyyar da su yayin da shirin zaɓen 2027 ke kankama.
3.John Odigie-Oyegun
John Odigie-Oyegun tsohon gwamnan jihar Edo ne kuma shi ne shugaban APC na farko a matakin ƙasa.
Ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar jam’iyyar a 2015, amma daga baya ya rasa tasiri sakamakon rikice-rikicen shugabanci.
4.Aminu Tambuwal
Aminu Tambuwal tsohon kakakin Majalisar Wakilai ne kuma tsohon gwamnan jihar Sakkwato, wanda a yanzu ke a matsayin Sanata.
An san shi da sauya jam’iyya daga APC zuwa PDP da sauransu. Ya sauya sheka zuwa ADC a ƴan kwanakin nan domin a haɗa ƙarfi wajen fitar da APC daga ofis.
5. Rauf Aregbesola
Rauf Aregbesola tsohon gwamnan Osun ne kuma tsohon ministan harkokin cikin gida. Ya taba kasancewa kusa da Bola Tinubu, amma daga baya suka samu sabani. Shigarsa ADC na nuni da neman sabon mafaka a siyasa bayan rikicin
6. Emeka Ihedioha
Emeka Ihedioha tsohon mataimakin kakakin Majalisar Wakilai ne kuma ya taba zama gwamnan Imo kafin kotu ta tsige shi.
Ya dade yana PDP, amma matsalolin siyasa sun shafi tafiyarsa. Daga baya ya sauya sheka zuwa ADC.
7. Babachir Lawal
Babachir Lawal ya taba zama sakataren gwamnatin tarayya a zamanin marigayi Muhammadu Buhari kafin a sauke shi.
Daga baya ya fara sukar APC. Yanzu yana daga cikin masu neman sabon dandali a ADC wanda ke da zazzafar adawa.
8. Dr. Mustapha Muhammad
Dr. Mustapha Muhammad jigo ne a siyasar Arewa, musamman a Katsina, inda yake da tasiri a matakin ƙasa da ƙasa.
Yana daga cikin masu goyon bayan Kwankwaso. Shigarsa ADC na da alaƙa da biyayya ga tafiyar Kwankwasiyya.
9. Kashim Ibrahim Imam
Kashim Ibrahim Imam ɗan siyasa ne daga jihar Borno wanda ya taba neman muƙamai daban-daban ciki har da gwamna.
Ya yi siyasa a jam’iyyu daban-daban kafin daga baya ya koma ADC a ƙoƙarin ci gaba da zama cikin sahun wajen fafutuka da jam'iyya mai mulki.
10. Lawal Daura
Tsohon Darakta janar na hukumar tsaro ta farin kaya ne shi, wato DSS. Ya bayyana aniyar neman takarar gwamnan jihar Katsina a zaɓen 2027.
11. Ahmad Babba Kaita
Ahmad Babba Kaita Sanata ne daga Katsina kuma yana daga cikin ‘yan PDP masu tasiri. Ya shahara wajen ayyukan majalisa da hulɗa da jama’a.
12. Rotimi Amaechi
Rotimi Amaechi tsohon gwamnan Rivers ne kuma tsohon ministan sufuri. Ya kasance jigo a APC kuma ya nemi takarar shugaban ƙasa a 2022.
13. Dino Melaye
Dino Melaye tsohon Sanata ne da aka fi sani da kaifin baki da bayyana ra’ayi. Ya kasance jigo a PDP kuma ya nemi gwamna a Kogi.
Wadannan mutane fitattu ne a siyasar Najeriya, wanda ake ganin za su iya kawo gagarumin canji a babban zaben 2027 da ke tunkaro Najeriya.
Ɗan Kwankwaso zai koma jam'iyyar ADC
A baya, mun wallafa cewa tsohon Kwamishina a Kano, Mustapha Rabi'u Musa Kwankwaso ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP bayan nazari mai zurfi.
Ya bayyana cewa a yanzu haka yana kan hanyar kammala shigar jam’iyyar hamayya ta ADC domin fara sabuwar tafiyar siyasa a jihar Kano da Najeriya a zaben 2027.
Ya bayyana cewa ADC na da damar kawo sauyi mai ma’ana a Kano da Najeriya bayan mahaifinsa ya koma can, yayin da ake ƙoƙarin haɗe kan yan adawa su fatattaki APC.
Asali: Legit.ng



