Ana Barazanar Hana ADC Taro a Abuja, Atiku Ya Fadi Matakin da za Su Dauka
- A yau Talata, 14 ga watan Yulin 2026 babbar jam'iyyar adawa ta ADC ta shirya gudanar da babban taronta na kasa domin zaben shugabanni
- Sai dai jam'iyyar ta ce mai wajen taron da suka karbi haya na fuskantar barazana daga jami'an gwamnati, lamarin da zai kawo musu cikas
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya fito ya yi magana kan matakin da jam'iyyar ADC za ta dauka duk da barazanar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC ta yi zargin cewa mai wurin da ta shirya gudanar da taronta yana fuskantar matsin lamba domin hana ta amfani da wurin, duk da cewa an kulla yarjejeniya tare da biyan kuɗi.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a jajiberin taron, jam’iyyar ta ce masu kula da Rainbow Event Centre sun sanar da ita cewa suna fuskantar matsin lamba mai tsanani.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Matsalar da aka samu a sulhun Amurka da Iran ya rusa burin 'yan Najeriya

Source: Facebook
Ana neman hana jam'iyyar ADC taro
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa ADC ta ce mai wajen taron ya ce yana fuskantar matsim lamba daga hukumar FCDA da kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, domin soke yarjejeniyar da suka yi.
A cewar ADC, an yi barazanar soke lasisin wajen taron idan har mai wajen ya bari jam’iyyar ta gudanar da taronta a yau Talata, 14 ga Yunin 2026.
Sanarwar ADC ta ce:
“Bayan mun biya duk kuɗin da ake bukata tare da kammala shirye-shirye domin taronmu, mai wurin ya sanar da mu cewa yana fuskantar matsin lamba daga FCDA da Ministan FCT,”
Matakin da ADC ta dauka
Sai dai jam’iyyar ta jaddada cewa tana da ingantacciyar yarjejeniya da wurin, kuma za ta gudanar da taronta kamar yadda aka tsara.
“Mun riga mun rattaba hannu kan yarjejeniya da shi. Za mu gudanar da taronmu gobe kamar yadda aka tsara a Rainbow Event Centre,”

Kara karanta wannan
Jagoran 'yan bindiga ya tura sako ga gwamnati, ya fadi matsayar sulhun da aka yi a Katsina
In ji sanarwar.
Jam’iyyar ADC ta bayyana wannan lamari a matsayin yunƙurin danne ‘yancin siyasa, tare da gargadi kan abin da ta kira “ƙaruwar mulkin kama-karya” a fagen siyasa.
“Ba za mu miƙa wuya ga wannan kama-karya ba. Kuma tabbas ba ga wannan ƙaramin mai mulkin danniya ba,”
In ji sanarwar, tana nuni kai tsaye ga gwamnatin birnin tarayya Abuja.
Maganar Atiku kan taron ADC
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku Abubakar ya sanar da cewa yi musu barazana alama ce da ke nuna dimokuradiyya na fuskantar koma baya.
Atiku Abubakar ya ce babu gudu ba ja da baya kan taron, kuma sun shirya kawar da gwamnatin Bola Tinubu a zaben 2027 mai zuwa.

Source: Facebook
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata amsa a hukumance daga FCDA ko ofishin Ministan Abuja kan zarge-zargen.
An nemi Tinubu ya ajiye Shettima
A wani labarin, mun kawo muku cewa an fara sabon kira ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ajiye Kashim Shettima a zaben 2027.

Kara karanta wannan
Muhimman abubuwa 5 da Amurka da Iran suka gaza warwarewa a zaman sulhu a Islamabad
Wata kungiya a jihar Bauchi ta nemi shugaban kasa Bola Tinubu da ya dauki gwamna Bala Mohammed domin takara tare da shi a zabe mai zuwa.
Ta kuma yi alkawarin yi wa tikitin Tinubu/Bala gangami na musamman domin tara musu mutane miliyan 10 da za su zabe su a 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng