'Ka Hakura da Takara': Baba Ahmed Ya Fadawa Atiku abin da Ya Kamata Ya Yi a 2027

'Ka Hakura da Takara': Baba Ahmed Ya Fadawa Atiku abin da Ya Kamata Ya Yi a 2027

  • Hakeem Baba-Ahmed ya shawarci Atiku Abubakar da ya hakura da neman shugabancin Najeriya, ya zama uban al'umma don ci gaban ƙasa
  • Baba-Ahmed ya ce ya kamata Atiku ya zama gwarzon dimokuraɗiyya a matsayinsa na jigon PDP kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa
  • Ya kuma buƙaci Atiku da ya mai da hankali kan samar da sababbin shugabanni, masu jini a jika, wadanda za su mulki Najeriya a madadin APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wani tsohon mai ba shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan siyasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana mahangarsa kan zaben 2027 da ke tafe.

Hakeem Baba-Ahmed, ya ba ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, shawara da ya hakura da takarar shugaban ƙasa a 2027.

Hakeem Baba-Ahmed ya bukaci Atiku Abubakar da ya hakura da neman shugabancin Najeriya
Hakeem Baba Ahmed ya nemi Atiku ya zakulo matasa masu jini a jika, ya dora su a shugabanci. Hoto: Atiku Abubakar, Hakeem Baba-Ahmed
Asali: Facebook

Tsohon hadimin Tinubu, kuma daya daga cikin dattawan Arewa, ya bayyana wannan ra'ayi ne yayin da yake hira da gidan talabijin AIT a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Ka hakura da takara' - Baba-Ahmed ga Atiku

Atiku, wanda ya riƙe muƙamin mataimakin shugaban kasa har tsawon shekaru takwas a zamanin mulkin Olusegun Obasanjo, ya fafata neman kujerar shugabancin Najeriya har sau uku.

Yayin da yake waiwaye kan tarihin siyasar Atiku, Hakeem Baba-Ahmed ya shawarci jagoran 'yan adawa a Najeriya da ya mai da hankali kan zama uban al'umma.

Hakeem Baba Ahmed ya bayyana cewa samun Atiku Abubakar a matsayin uban al'umma, zai fi zama abu mai muhimmanci a Najeriya, fiye da ci gaba da neman mulki.

Tsohon hadimin Tinubun ya ce:

"Kai fitaccen dan jam'iyyar PDP ne, kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa ta. Ka yi mataimakin shugaban kasa na shekaru takwas, kuma ka nemi shugabancin ƙasa sau uku.
"Ina ganin ya kamata ka zama gwarzon dimokuraɗiyya, amma ba na jin ya kamata ka sake neman shugabancin wannan ƙasar."

Hakeem Baba-Ahmed ya ce ya kamata su El-Rufai da Amaechi su hakura da neman shugabanci, su kyale matasa su yi
Hakeem Baba-Ahmed, tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa. Hoto: Hakeem Baba-Ahmed
Asali: Twitter

Baba Ahmed ya tabo su El-Rufai, Amaechi

Hakeem Baba Ahmed ya ƙara da cewa:

"Ya kamata ya zama uban al'umma. Ya kamata ya zamo jagora a wajen samar da gwamnatin wata jam'iyyar da za ta maye gurbin APC.
"Ya kamata ya kawo sababbin jini, masu sababbin ra'ayoyi, ya dauko sababbin mutane, sannan zama madubinsu da zai haska masu yadda za su yi shugabanci."

Ya kuma shawarrci Rotimi Amaechi da ya yi hakan, tare da Nasir El-Rufai, "idan yana ganin zai iya sarrafa girman kansa," ya zama wani ɓangare na wannan shirin.

Ba wannan ne karon farko da Hakeem Baba Ahmed yake kira ga Atiku da ya kura da takara ba, ko a watan Mayun 2025 sai da ya yi irin wannan kira.

Kalli tattaunawar a nan kasa:

Baba-Ahmed ya nemi Tinubu ya hakura da tazarce

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya bukaci Atiku Abubakar da ya hakura da takarar shugaban kasa, ya ba matasa dama su jagoranci Najeriya.

Tsohon hadimin shugaban kasar, ya gargadi Bola Tinubu da kada ya nemi tazarce a 2027, yana mai bayyana wasu dalilai na rashin dacewar hakan.

Hakeem Baba-Ahmed ya ce ya kamata ‘yan takarar da suka tsufa su yi murabus daga siyasa, ko kuma ‘yan Najeriya su yi masu ritayar dole.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.