Duk da Kwankwasiyya Ta Bar NNPP, Jam'iyyar na Ci gaba da Kuka da INEC

Duk da Kwankwasiyya Ta Bar NNPP, Jam'iyyar na Ci gaba da Kuka da INEC

  • 'Daya daga cikin jam’iyyar adawa a Najeriya NNPP ta sake rubuta wa hukumar zabe ta kasa, INEC wasika tana neman ta bi hukuncin kotu a cikin gaggawa
  • Jam’iyyar ta nuna damuwa kan jinkirin da ya wuce makonni uku ba tare da martani ba daga hukumar zaben duk da kotu ta nemi a amince da shugabancinta
  • NNPP ta kuma nemi a shirya ganawa domin warware sabanin da ke tsakaninsu yayin da siyasar Najeriya ke ci gaba da daukan zafi kafin zaben 2027

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos– Jam’iyyar NNPP ta sake aika wasika ga hukumar zabe ta kasa, INEC, tana buƙatar ta gaggauta bin wani hukuncin kotu tare da neman a shirya ganawa domin tattauna matsalar rashin bin umarnin da ta ce hukumar ta yi.

Kara karanta wannan

SERAP ta nemi majalisa ta bi diddigi, ta binciki alaƙar shugaban INEC da APC

A cikin wasikar da aka rubuta ranar 13 ga Afrilu, 2026, wacce aka aika ga shugaban INEC tare da kwafe zuwa ga daraktan shari’a, jam’iyyar ta bakin lauyoyinta na Lex Firma LP ta bayyana damuwa kan hukumar.

NNPP ta zargi INEC da take shari'a
Shugaban hukumar INEC ta kasa, Joash Amupitan Hoto: @NGRSenate
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa NNPP ta damu domin ta ce fiye da makonni uku bayan hukuncin babbar kotun tarayya, har yanzu hukumar ba ta ɗauki wani mataki ba.

NNPP ta rubuta wa INEC takarda

Jaridar The Sun ta wallafa cewa jam’iyyar ta tuna cewa tun da farko ta rubuta wa INEC a ranar 24 ga Maris, 2026, tana sanar da ita hukuncin da aka yanke a ranar 17 ga Maris, 2026 tare da neman a bi umarnin cikin sa’o’i 72 kamar yadda kotu ta umarta.

NNPP ta nemi zama da INEC
Shugaban hukumar INEC a ganawarsa da manema labarai Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Wasikar ta ce:

“Abin takaici ne cewa duk da bayyanannun umarnin kotu na bin hukunci cikin sa’o’i 72, fiye da makonni uku sun shude ba tare da wani martani daga hukumar ba."
“Ba a ɗauki wani mataki don aiwatar da hukuncin ba, haka kuma babu wata sanarwa a hukumance da aka bai wa wakilanmu da ke bayyana matsayin hukumar.”

NNPP ta soki INEC kan hukuncin kotu

Kara karanta wannan

Ana barazanar hana ADC taro a Abuja, Atiku ya fadi matakin da za su dauka

NNPP ta bayyana wannan hali a matsayin abin damuwa matuƙa, musamman duba da ficewar Dr. Ajuji Ahmed da abokan tafiyarsa zuwa jam’iyyar ADC, tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Jam’iyyar ta ce abin mamaki ne yadda INEC ke ci gaba da ƙin amincewa da sahihin shugabancin NNPP, yayin da ake ganin tana bai wa wasu da suka fice daga jam’iyyar karɓuwa.

NNPP ta kuma soki abin da ta kira rashin mutunta ikon kotu, tana gargadin cewa hakan na iya kawo illa ga bin doka da oda a ƙasar.

Ta ce:

“Ra’ayin cewa wani mutum ko hukuma za su iya watsi da ingantaccen hukuncin kotu ko kuma su fassara shi yadda suke so ba tare da bin ka’ida ba, abu ne mai tayar da hankali kuma ba ya yi wa tsarin mulkin ƙasa da bin doka adalci."

Kwankwaso ya bar jam'iyyar NNPP

A baya, mun wallafa cewa tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tabbatar da yin murabus daga daga jam’iyyar NNPP mai adawa bayan tsawon lokaci ana gwabzawa.

Kwankwaso ya bayyana wannan mataki da ya dauka a matsayin mai wahala, yana mai cewa sauyin siyasa a kasa ya tilasta masa hakan domin a nema wa talakawan Najeriya sauki daga halin da suke ciki.

'Dan siyasar ya sauya sheka zuwa jam'iyyar hadakar yan hamayya ta ADC, inda ya bayyana cewa za a yi tafiya tare domin a kifar da gwamnati mai ci a karkashin Bola Tinubu da APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng