SERAP Ta Nemi Majalisa Ta Bi Diddigi, Ta Binciki Alaƙar Shugaban INEC da APC
- Ƙungiyar SERAP ta nemi majalisar dokokin Najeriya ta fara cikakken bincike kan zargin da ya shafi shugaban INEC, Joash Amupitan
- A cikin ƴan kwanakin nan, an tono waɗansu sakonnin da ake zargin Amupitan ya wallafa su da ke nuna goyon baya ga APC goyon baya
- SERAP ta bayyana cewa dole ne a yi taka tsan-tsan domin lamarin na iya shafar amincewar jama’a da sahihancin zabe a Najeriya mai zuwa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja– Kungiyar kare hakkin jama’a da yaki da rashawa ta SERAP ta bukaci majalisar dokoki ta kasa da ta fara cikakken bincike kan zarge-zargen da suka shafi shugaban INEC.
A ƴan kwanakin nan ne aka gano wasu sakonnin goyon bayan APC a kafafen sada zumunta da ake dangantawa da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan.

Source: Twitter
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta wallafa a shafinta na X ranar Litinin, 13 ga watan Afrilu, 2026 SERAP ta roki ‘yan majalisar da su yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba su wajen gudanar da bincike.
SERAP na son a binciki shugaban INEC
Kungiyar ta bayyana cewa batun ba wai kawai rikici ne na kafafen sada zumunta ba, illa yana da alaka da sahihanci da kuma yadda ake kallon hukumar zabe ta INEC a idon jama’a.
SERAP ta ce:
“Amincewa da INEC abu ne mai matukar muhimmanci ga sahihanci da ingancin tsarin zabe a Najeriya, don haka duk wani zargi da zai iya kawo tangarda ga wannan amincewa dole ne a bincike shi cikin gaggawa, sosai, a bude kuma cikin gaskiya.”
SERAP ta kuma jaddada cewa majalisar dokoki tana da cikakken iko a karkashin sashe na 88 da 89 na kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima na binciken ayyukan hukumomi da jami’an gwamnati domin gano rashawa, gazawa ko cin zarafin iko.

Kara karanta wannan
APC: Tsohon saƙon shugaban INEC ya jawo zazzafar muhawara kan sahihancin zaben 2027

Source: Twitter
A cewar SERAP:
“Babu wani jami’i ko hukuma da ta fi karfin a bincike ta, kuma wajibi ne majalisar dokoki ta tabbatar da cewa ba a yi watsi da zarge-zarge ko boye su ba.”
SERAP ta tunawa majalisa karfin ikonta
Kungiyar ta kuma bayyana cewa ‘yan majalisar na da nauyi a karkashin dokokin kasa da kasa na kare hakkin dan Adam.
Daga ciki har da yarjejeniyar Afrika kan hakkin dan adam da yarjejeniyar duniya kan ‘yancin dan adam da siyasa, wadanda ke wajabta tabbatar da gaskiya, rikon amana da adalci a shugabanci.
SERAP ta ce duk wani bincike da za a gudanar dole ne ya bi ka’idojin doka da bai wa kowa damar kare kansa, sannan a bayyana sakamakon ga jama’a domin dawo da amincewa da tsarin zabe.
Ta kara da cewa bayyana gaskiyar sakamakon binciken yana da matukar muhimmanci wajen tabbatar da rikon amana da kuma sake gina yarda da tsarin zabe.

Kara karanta wannan
DSS ta gano tsohon 'dan majalisa da ya kada hantar Amurka da rashin tsaro a Najeriya
Kungiyar ta yi gargadin cewa rashin daukar mataki kan irin wadannan zarge-zarge na iya kara rage amincewar jama’a da INEC gabanin zabuka masu zuwa.
Tsofaffin sakonnin Amupitan sun yamutsa hazo
A baya, kun ji cewa tsohon sakonnin da ake dangantawa da shugaban INEC, Joash Amupitan sun tayar da sabon rikici a kan babban zaɓe mai zuwa a 2027.
Duk da yunƙurin da fitaccen mai sharhi, Farouk Kperogi ya yi na binciko saƙon, hukumar INEC ta ce ƙarya ake yi wa Amupitan domin ba shi da asusu a shafin X.
Ƴan Najeriya sun rabu kan sahihancin zargin da tasirinsa ga amincewa da zaɓe zuwa ganin alaƙar da ake zargin yana da ita da APC mai mulkin Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
