APC Za Ta Ci Gaba da Raunata 'Yan Adawa, Yilwatda Ya Fadi Manyan ADC da Za Su Koma Jam'iyyar

APC Za Ta Ci Gaba da Raunata 'Yan Adawa, Yilwatda Ya Fadi Manyan ADC da Za Su Koma Jam'iyyar

  • Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya gudanar da taro da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a jihar Plateau
  • Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa jam'iyyar tana yayi a halin yanzu, 'yan adawa ke rububin shigowa cikinta
  • Hakazalika ya bada tabbacin cewa wasu fitattun mutane daga jam'iyyar ADC za su tattara kayansu zuwa APC mai mulki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi magana kan sauya shekar da ake yi zuwa jam'iyyar.

Farfesa Nentawe ya bayyana cewa karin ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa za su koma APC a kwanaki masu zuwa.

Shugaban APC ya ce 'yan ADC za su koma jam'iyyar
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: Prof. Nentawe Yilwatda
Source: Twitter

Jaridar The Nation ta ce Yilwatda ya bayyana hakan ne a lokacin taron da ya gudanar da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na jihar Plateau a otal din Crest da ke birnin Jos, a ranar Juma'a, 17 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan

"Ta fi komai": Gwamna Makinde ya fadi sauya shekar mai muhimmanci ga 'yan Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da yake neman afuwa kan jinkirin zuwansa wurin taron, Farfesa Yilwatda ya ce hakan ya samo asali ne daga taron da ya halarta a jihar Kebbi tare da gwamnonin APC domin tantance halin da jam’iyyar ke ciki.

Wane hali jam'iyyar APC take ciki?

Farfesa Yilwatda ya tabbatarwa mambobin jam’iyyar cewa APC tana cikin koshin lafiya, kuma babu abin da ke damunta, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar da labarin.

"Ba wata kwayar cuta ko ta kwayoyin halitta da ta kama jam’iyyar. Har ma mun kai ta dakin gwaji a Kebbi, kuma sakamakon ya fito lafiya lau!”

- Farfesa Nentawe Yilwatda

Jiga-jigan ADC za su koma APC

Shugaban jam’iyyar ya kuma bayyana cewa APC za ta karɓi wasu sababbin masu sauya sheka daga jam’iyyar ADC a mako mai zuwa.

“A mako mai zuwa, zan karɓi wasu fitattun mutane daga ADC."
“Wasu daga cikin wadanda suka bar PDP zuwa ADC yanzu za su dawo APC."

Kara karanta wannan

Diri: Jam'iyyar APC ta fara zawarcin gwamnan da ya fice daga PDP, ta bayyana dalili

“Yawancinsu sun kammala ‘gwajin lafiya’ kuma za a bayyana su a hukumance nan da mako mai zuwa.”
"Wani daga cikin masu sauya shekar ya yi kokarin bayyana kansa kwanan nan, kuma watakila kun gani a labarai, amma za mu karɓe shi a hukumance nan ba da jimawa ba.”
“Mutane da yawa suna shigowa, ’yan majalisa, gwamnoni, da sanatoci. APC ita ce amaryar siyasa a wannan lokaci.”

- Farfesa Nentawe Yilwatda

Jiga-jigan ADC za su koma APC
Farfesa Nentawe Yilwatda tare da shugabannin APC Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

Farfesa Yilwatda ya yi godiya

Hakazalika ya gode wa mambobin jam’iyyar bisa goyon bayan da suka nuna masa lokacin da mahaifiyarsa ta rasu kwanan nan.

“Lokacin da na rasa mahaifiyata, dukan iyalan APC, musamman na Plateau, sun tsaya tsayin daka tare da ni."
“Kun ba ni kafada da zan jingina, kun zama ginshiki mai karfi a gare ni a lokacin da na fi bukatar taimako."
“Hawayena sun daina gudu saboda kun kasance tare da ni don ba ni tausayawa da goyon baya.”

- Farfesa Nentawe Yilwatda

PDP ta fadi dalilin gwamnoninta na komawa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta yi magana kan sauya shekar da gwamnoninta ke yi zuwa APC.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamna Bago ya samo hanyar magance 'yan ta'adda

Jam'iyyar ta ragargaji gwamnoni da suka fice daga cikinta, tana cewa sun yi hakan ne saboda son kai da kwadayi, ba don wani dalili mai tushe ba.

Hakazalika, ta ce ba gwamnoni ke gina jam’iyya ba, mutane ne keyin hakan, inda ta nuna cewa za su gane kuskurensu kafin zaben 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng