Rashin Tsaro: Gwamna Bago Ya Samo Hanyar Magance 'Yan Ta'adda

Rashin Tsaro: Gwamna Bago Ya Samo Hanyar Magance 'Yan Ta'adda

  • Matsalar rashin tsaro na ci gaba da addabar sassa daban-daban na Najeriya, inda 'yan bindiga da 'yan ta'adda ke cin karensu babu babbaka
  • Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya bukaci a sare dazuzzukan da 'yan ta'addan ke boyewa
  • Ya nuna cewa bai kamata a ce akwai dazuzzuka ba yayin da ake korafi kan matsalar yunwa a tsakanin al'umma

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.

Gwamna Bago ya bukaci a mayar da dazuzzuka da gandun dajin da 'yan ta'adda ke boyewa zuwa manyan gonaki domin samar da wadataccen abinci a kasa.

Gwamna Bago ya bukaci a sare dazuzzuka
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago. Hoto: @HonBago
Source: Twitter

Jaridar The Nation ta ce Gwamna Bago ya bayyana haka ne jiya a cibiyar NIIA da ke Legas, yayin da yake magana a matsayin babban bako mai gabatar da jawabi a bikin tunawa da ranar abinci ta duniya ta 2025.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun lallaba cikin masallaci ana sallar asuba, sun sace mutane

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace shawara Gwamna Bago ya bada?

Ya ce akwai bukatar gwamnati ta zuba jari wajen gyara kasa, shirya ta don noma, da kuma inganta kayayyakin gona domin habaka tattalin arziki da rage yunwa.

“Idan ka yi tafiya zuwa kasashen waje, ka hau jirgin kasa, idan ka duba hagu, za ka ga kasar da aka gyara, idan ka duba dama, haka ma. Wannan ba haɗari ba ne, ana sane aka yi hakan."
“Ana magana kan rashin tsaro da ’yan bindiga a cikin daji. Amma me ya sa muke da daji? Mutane na fama da yunwa amma suna son barin daji haka kawai."
"Mu sare dajin, mu maida shi gonaki, mutane su samu arziki. Mu ga inda masu laifi za su ɓuya. Amma idan aka bar daji, zai ci gaba da zama daji.”
Gwamna Bago ya bayyana cewa ya taba gayyatar babban hafsan tsaro ya zo jiharsa don samun hekta 100,000 domin kafa gonar sojoji.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kebbi ta jawo kamfanin kasar China domin taya ta yaki da Lakurawa

“Na kuma gaya wa ’yan sanda su zo su samu hekta 100,000 a inda ake da matsalar tsaro. Ku kawo manyan motocin yaki, ku kafa gona, domin sojojin ku su ci abincin da suka noma da kansu."

- Gwamna Umaru Bago

Gwamna Bago ya yi magana kan rashin tsaro
Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Neja. Hoto: @HonBago
Source: Twitter

Gwamna Bago ya bukaci a sare dazuzzuka

Gwamna Bago ya ce bai dace Najeriya ta ci gaba da barin dazuzzuka ba, inda ’yan ta’adda ke ɓuya.

“Bai kamata mu ci gaba da barin dazuzzuka inda 'yan Boko Haram da sauran masu laifi ke buya. Daga Legas zuwa Ibadan, yawan dajin da ke gefen hanya yana tayar da hankali. Mu share su."
"Idan kuma muna son dazuzzuka, to mu tsara su ta yadda ba za su zama mafaka ga masu laifi ba."

- Gwamna Umaru Bago

'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun shiryawa jami'an tsaro kwanton bauna a jihar Zamfara.

'Yan bindigan sun hallaka jami'an tsaro guda takwas da suka hada da 'yan sanda da jami'an rundunar Askarawan Zamfara.

Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan bindigan sun yi wa jami'an tsaron kwanton bauna ne lokacin da suke aikin sintiri.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng