"Ta Fi Komai": Gwamna Makinde Ya Fadi Sauya Sheka Mai Muhimmanci ga 'Yan Najeriya
- Yawan sauya shekar da 'yan siyasa ke yi daga wannan jam'iyya zuwa wancan na ci gaba da daukar hankali a Najeriya
- Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa har yanzu ba a yi sauya shekar da tafi muhimmanci ga 'yan Najeriya ba
- Makinde ya nuna cewa bai kamata batun sauya sheka ya dauke hankalin mutane kan wahalar da 'yan Najeriya suke sha ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi magana kan yawan sauya shekar da 'yan siyasa ke yi daga wannan jam'iyya zuwa wancan.
Gwamna Seyi Makinde ya ce sauya sheka ɗaya tilo da take da muhimmanci, ita ce ranar da yunwa da talauci za su bar kasar nan.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ce Makinde ya bayyana haka ne ranar Alhamis a cikin wasikar da yake fitarwa kowane wata.

Kara karanta wannan
Diri: Jam'iyyar APC ta fara zawarcin gwamnan da ya fice daga PDP, ta bayyana dalili
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Makinde ya ce kan sauya sheka?
Gwamna Makinde yana mayar da martani ne kan yawan sauya sheka da gwamnoni da ‘yan siyasa ke yi daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
“Na tabbata da yawa daga cikinku kuna bin labaran sauya shekar ‘yan siyasa, musamman gwamnoni da suka bar PDP zuwa APC da sauran jam’iyyu."
“Amma a gare ni, sauya sheka ɗaya ce kawai da take da muhimmanci, wadda bata faru ba tukuna, sauya shekar yunwa.”
- Gwamna Seyi Makinde
Gwamnan ya ce ’yan Najeriya sun fi damuwa da lokacin da wahalar tattalin arziki da tsadar rayuwa za su “sauya sheƙa” daga rayuwarsu, maimakon bin labaran siyasar jam’iyyu, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar da labarin.
“Na bayyana a taron manema labarai kwanan nan cewa, ‘zan damu ne kawai idan yunwa ta sauya sheka zuwa APC.’ Na fadi hakan ne da gaske."
- Gwamna Seyi Makinde
Makinde ya koka kan tsadar rayuwa
Ya nuna damuwa cewa yayin da ’yan siyasa ke ta sauya jam’iyya, talakawa kuwa na fama da tsadar rayuwa da rashin abinci.
“Ba za mu ci gaba da nuna kamar komai lafiya yake ba saboda wani a gwamnati ya ce haka ba. Abin da ke faruwa shi ne gibin rashin daidaito yana faɗaɗa. Masu kuɗi suna kara samun sakewa, amma talakawa suna nutsewa cikin wahala."
- Gwamna Seyi Makinde

Source: Facebook
Gwamna Makinde ya yi nuni da cewa 'yan Najeriya ne kadai ba 'yan siyasa ko masana kan siyasa bane za su taka rawar gani wajen yadda sakamakon zaben 2027 kasance.
“A karshe, ba ’yan siyasa ko masu dabarun zaɓe za su yanke hukunci ba — ’yan Najeriya ne za su tantance wanda ya cancanta ya jagorance su a 2027."
- Gwamna Seyi Makinde
Sanatan PDP ya koma jam'iyyar APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanatan da ke wakiltar Bayelsa ta Tsakiya a majalisar dattawa, Benson Konbowei, ya fice daga jam'iyyar PDP.
Sanata Benson Konbowei ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC bayan ya raba gari da PDP mai adawa a Najeriya.
Ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da suka addabi PDP na daga cikin dalilan da suka sanya ya fice daga jam'iyyar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

