Ba Tare da Boye Boye ba, PDP Ta Fadi dalilin da Ya Sa Gwamnoninta Komawa APC

Ba Tare da Boye Boye ba, PDP Ta Fadi dalilin da Ya Sa Gwamnoninta Komawa APC

  • Jam’iyyar PDP ta yi magana game da yawan sauya sheka da ake yi musamman daga cikinta zuwa APC mai mulkin Najeriya
  • PDP ta zargi gwamnoni da suka fice daga cikinta da son kai da kwadayi, tana cewa za su gamu da sakamakon su a 2027
  • Kakakin PDP, Ibrahim Abdullahi, ya ce jam’iyyar ta shirya sosai duk da kalubale, kuma ta mayar da hankali kan babban taronta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta yi martani kan gwamnonin da ke barinta zuwa APC.

Jam'iyyar ta soki gwamnoni da suka bar ta, tana cewa sun yi hakan ne saboda son kai da kwadayi, ba don wani dalili mai tushe ba.

PDP ta soki gwamnoni da suka koma APC
Shugaban PDP, Umar Damagum da Bola Tinubu. Hoto: Official People's Democratic Party, PDP, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Mataimakin kakakin PDP na ƙasa, Ibrahim Abdullahi, ya bayyana cewa ficewar gwamnonin ba wata hujja sai son kai da kwaɗayi kawai, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa bai kamata Jonathan ya yi kuskuren neman takara a 2027 ba'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda PDP ta rasa kusoshi bayan zaben 2023

Tun bayan zaben 2023, gwamnoni hudu sun bar PDP, ciki har da na Delta, Akwa Ibom, Enugu da kuma Bayelsa a wannan makon.

Haka kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da abokin takararsa Ifeanyi Okowa sun fice daga jam’iyyar tare da wasu manyan abokansu.

PDP ta karfafawa ƴaƴanta guiwa a jam'iyyar

Jam’iyyar ta ce ba gwamnoni ke gina jam’iyya ba, mutane ne ke hakan, tana mai cewa za su gane kuskurensu kafin zaben 2027.

Ya ce jam’iyyar tana cikin koshin lafiya duk da ƙalubale, kuma ta gyara matsalolin da za su hana ta zama babbar mai adawa a 2027.

PDP ta caccaki gwamnoni da ke komawa APC
Shugaban PDP, Umar Damagum. Hoto: Official People's Democratic Party, PDP.
Source: Twitter

'Ko a jikinmu' - PDP kan sauya sheka

Abdullahi ya ƙara da cewa PDP ba ta damu da ficewar gwamnoni ba, domin tana shirye-shiryen babban taronta na ƙasa a Ibadan.

Kara karanta wannan

Bayan murabus din Gwamna Diri, Sanatan PDP ya koma jam'iyyar APC

Ya ce waɗanda suka bar jam’iyyar suna da son kai kuma hakan ya ba PDP damar “tsaftace” kanta daga miyagu kafin babban taron, cewar rahoton Daily Post.

Abdullahi ya soki gwamna Peter Mbah da cewa bai taɓa zuwa manyan tarurrukan PDP a Abuja ba tsawon shekaru hudu da ya shige.

Ya kuma caccaki tsohon gwamnan Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi, da cewa ya rage martabarsa ta siyasa har ya koma “mai ɗaukar jakar” minista.

Zargin da ake yi wa jam'iyyar APC

Jigo a PDP, Samuel Ogidi daga yankin Kudu maso Kudu ya ce gwamnoni da mambobin PDP suna fuskantar matsin lamba daga APC su bar jam’iyyar.

Ya ce ana tilasta musu su koma APC don a maida Najeriya jam’iyya ɗaya, amma PDP za ta ci gaba da shirye-shiryenta na taron Ibadan.

Sanatan PDP ya koma APC a Bayelsa

Kun ji cewa jam'iyyar mai adawa a Najeriya ta sake samun koma baya a majalisar dattawa bayan ficewar daya daga cikin sanatocinta.

Sanata Benson Konbowei mai wakiltar Bayelsa ta Tsakiya ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai rinjaye.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Matsala ta tunkaro Gwamna Diri kan ficewa daga PDP

Ya bayyana cewa babu wani dan siyasan da ya san abin da yake yi da zai ci gaba da zama har sai PDP ta warware rikicinta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.