"Akwai Matsaloli': Amupitan Ya Fadi Shirinsa kan Amfani da BVAS a Zabukan Najeriya
- Sabon Shugaban INEC na kasa, Farfesa Joash Amupitan ya ce zai duba tsarin amfani da fasaha a harkokin zaben Najeriya
- Ya bayyana haka ne ga taron majalisa yayin da ake tantance shi a matsayin sabon Shugaban Hukumar Zabe na kasa
- Amupitan ya bayyana cewa duk da tsarin BVAS na kokarin inganta zabe, amma akwai matsalolin da dama a amfani da fasahar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Sabon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya bayyanaabin da zai fara mayar da hankali a kai.
Ya bayyana cewa idan aka tabbatar da nadinsa har ya shiga ofis, zai duba yadda ake amfani da fasaha a tsarin zabe na Najeriy.

Source: Facebook
AIT ta wallafa cewa ya bayyana haka a yayin da yake magana a gaban majalisar dattawa, yayin tantance shi a ranar Alhamis, 16 ga watan Oktoba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amupitan ya magantu kan BVAS
The Nation ta wallafa cewa Farfesa Amupitan ya ce an kirkiro da tsarin BVAS ne domin kara inganci da sahihanci zabukan kasar nan.
Amma ya jaddada cewa sakamakon zaben 2023 ya nuna cewa akwai matsaloli da ya kamata a magance kafin a ci gaba da amfani da tsarin.
Amupitan ya ce duk da an samar da BVAS ne don tabbatar da sahihanci bayanan zabeu, amma daga baya kotun koli ta ce ba a aminta da shi ba a dokar kasa.
Don haka, ya ce yana da niyyar sake nazari a kan tsarin fasahar baki dayansa domin gano kurakurai da inganta shi nan gaba.
Amupitan: Zan hada kai da kungiyoyi
Baya ga batun fasaha, Farfesa Amupitan ya bayyana cewa jigilar kayan zabe na daga cikin manyan matsalolin da ke hana zabe tafiya yadda ya kamata.

Source: Twitter
Ya ce dogaro da kamfanoni masu zaman kansu wajen jigilar kayayyakin sirri na zabe na janyo jinkiri da kuma sakamako maras tabbas.
Ya jaddada cewa a karkashin jagorancinsa, INEC za ta fi maida hankali wajen tsara dabarun aikawa da kayan zabe da wuri.
Farfesa Joash Amupitan ya ce za a yi haka ne da hadin kai tsakanin hukumomin gwamnati kamar EFCC da kamfanonin sadarwa.
A ganinsa, hakan zai tabbatar da cewa duk wata fasaha da za a yi amfani da ita, ta samu amincewar jama’a yadda ya kamata.
Ya ce dole ne fasahar zabe ta kasance mai saukin amfani da kuma kariya daga duk wata barazana ga sahihancin sakamakon zabe.
An yi kuka da BVAS
Salamatu Ahmad, tsohuwar daliba ce da ta taɓa aikin zabe a daya daga cikin kananan hukumomin jihar Kano.
Ta shaida wa Legit cewa dama ana fama da na'urar a lokacin da su ka yi amfani da ita a yayin tantance masu kada kuri'a.
"Wasu lokutan sai mu yi yi, amma ba ta daukar bayanai yadda ya dace, masu zuwa zaɓen su yi ta jin haushi."
Ta ce mika idan aka duba na'urar aka yi wasu gyare-gyare, za a samu saukin matsalolin da ta ke zuwa da su a lokacin zabe.
Majalisa ta cimma matsaya kan Amupitan
A baya, kun ji cewa Majalisar Dattawa ta Najeriya ta tabbatar da Farfesa Joash Ojo Amupitan, SAN, a matsayin sabon shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).
Wannan tabbaci ya biyo bayan zaman tantancewa da ya ɗauki kusan sa’o’i biyu a zauren majalisar dake babban birnin tarayya a ranar Alhamis, 16 ga watan Oktoba, 2025.
A yayin wannan tantancewa, sanatoci sun yi masa tambayoyi masu muhimmanci game da manufofinsa, yadda zai tsara gudanar da harkokin INEC da tabbatar da sahihancin zabe.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


