Majalisa na Shirin Cika Burin Tinubu, Za Ta Tantance Sabon Shugaban INEC, Amupitan
- A yau Alhamis, 16 ga watan Oktoba, 2025 ne Majalisar Dattawan Najeriya za ta zauna da sabon Farfesa Joash Ojo Amupitan
- Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ne ya aika wa Majalisa da wasika, yana neman su amice da Amupitan a matsayin Shugaban INEC
- Shugaban kasa da sahalewar Majalisar Koli sun amince Farfesa Joash Amupitan ya zama sabon Shugaban Hukumar Zaben kasar nan
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Majalisar Dattawa ta bayyana cewa za ta tantance Farfesa Joash Ojo Amupitan a yau, Alhamis 16 ga Oktoba 2025.
Za ta yi wannan tantancewa ne domin tabbatar da nadinsa a matsayin sabon Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC).

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa wannan ya biyo bayan wasikar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da aka karanta a zauren majalisa a ranar Laraba.

Kara karanta wannan
Majalisa ta fara binciken yadda $35m da aka ware don gina matatar mai ta yi layar zana
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya aika wasika ga majalisa
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa Shugaba Tinubu ya bukaci majalisa da ta duba nadin cikin gaggawa bisa tanadin Sashe na 154 (1) na Kundin Tsarin Mulki na 1999.
A wata sanarwa da Bullah Audu Bi-Allah, Daraktan Harkokin Yada Labarai na Majalisar Dattawa ya fitar, ya tabbatar da tantancewar a yau.
Ya bayyana cewa tantancewar za ta gudana a dakin majalisar da ke cikin ginin Majalisar Tarayya, Abuja, kuma za a gayyaci manema labarai don daukar zaman kai tsaye.
Nadin Farfesa Amupitan ya biyo bayan kammala wa’adin Farfesa Mahmood Yakubu wanda ya jagoranci hukumar INEC na tsawon shekaru 10.
Nadin da Tinubu ya yi wa Amupitan ya haddasa ce-ce-ku-ce daga wasu kungiyoyi da ‘yan adawa da ke bukatar tantancewar ta zama mai gaskiya da adalci.
‘Yan Arewa sun goyi bayan nadin Tinubu
Kungiyar Northern Nigeria Minorities Group (NNMG) ta bayyana goyon bayanta ga nadin Farfesa Amupitan, inda ta ce bai kamata a siyasantar da sa kabila a batun ba.

Kara karanta wannan
Atiku: "Gaskiya ta fito da ministan Tinubu ya tona asiri kan kwangilar Legas zuwa Kalaba

Source: Facebook
A wata sanarwa da Chief Jacob Edi, jagoran kungiyar ya fitar a Kaduna, ya koka da yadda wasu ke kokarin nuna nadin a matsayin al’amarin wariya ko fifita wani yanki.
Ya ce:
“Wannan shi ne karon farko cikin shekaru 65 da wani daga kabilun Arewa marasa rinjaye zai zama shugaban hukumar INEC.”
“Ya kamata a yaba da nadin a matsayin cigaba wajen wakilci da adalci a shugabancin kasa.”
Ya kara da cewa yunkurin rage kimar nadin saboda asalin Amupitan daga yankin Okun a jihar Kogi ba wai kawai rashin adalci ba ne, illa ce ga hadin kan kasa.
Edi ya kuma jaddada cewa nadin Amupitan ya nuna cewa Shugaba Tinubu yana kokarin wakiltar kowa da kowa a cikin al’ummar Najeriya.
ADC ta aika sako da Amupitan
A baya, mun wallafa cewa jam’iyyar ADC ta fito fili tana kiran sabon shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan, da ya kasance mai gaskiya,
A wata tattaunawa da Malam Bolaji Abdullahi, mai magana da yawun ADC na ƙasa ya bayyana cewa ba su da cikakken sani a kan mutumin da Bola Tinubu ya nada shugabancin INEC.
Jam’iyyar ADC ta ce irin wannan nadin ya bai wa Amupitan wata babbar dama a tarihi, amma kuma wannan dama ce da ke ɗauke da nauyi, tunda al’umma na sa ido sosai.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
