'Za a Yi Sahihin Zaben da Kowa zai Yarda da Shi a 2027,' Shugaban INEC

'Za a Yi Sahihin Zaben da Kowa zai Yarda da Shi a 2027,' Shugaban INEC

  • Sabon shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce zai tabbatar da sahihin zabe da zai sa wadanda suka fadi su yarda da sakamako
    Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin Amupitan bayan ta masa tambayoyi masu tsawo kan shirin da yake da shi a hukumar INEC ta kasa
    Amupitan ya bayyana cewa ba ya da wata alaka da jam’iyyun siyasa ko kuma shari’ar zaben shugaban kasa da ta gabata a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.


FCT, Abuja – Sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya ce zai gudanar da sahihin tsarin zabe a karkashin jagorancinsa.

Farfesa Amupitan ya zaben zai kasance wanda zai tabbatar da gaskiya da adalci ga kowa da kowa a Najeriya.

Sabon shugaban INEC a Najeriya
Shugaban INEC da majalisa ta tantance, Farfesa Amupitan. Joash Ojo Amupitan
Source: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa ya bayyana hakan ne a gaban majalisar dattawa, inda ya ce burinsa shi ne samar da tsarin zabe mai inganci.

Amupitan zai karbi ragamar hukumar daga hannun tsohon shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya kammala wa’adin shekaru 10 a ranar 7, Oktoba, 2025.

Kara karanta wannan

"Akwai matsaloli': Amupitan ya fadi shirinsa kan amfani da BVAS a zabukan Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban INEC ya ce zai yi sahihin zabe

Yayin da yake amsa tambayoyi a gaban Majalisar Dattawa, Farfesa Amupitan ya ce zai yi aiki tare da hukumomi kamar hukumar NIMC da NCC domin tabbatar da ingantaccen tsarin zabe a Najeriya.

Punch ta wallafa cewa ya ce:

“Manufarmu ita ce mu tabbatar da sahihin zabe da kowa zai yarda da shi, kamar yadda alkalin kotu ke yanke hukunci cikin adalci da gaskiya.”

Sabon shugaban hukumar ya ce zai tabbatar da cewa fasahar zamani ta taimaka wajen tabbatar da gaskiya a dukkan zabubbuka da hukumar za ta gudanar a nan gaba.

Amupitan ya bayyana cewa saboda ingancin zaben da zai gudanar, duk wanda ya fadi zai taya wanda ya lashe zaben murna.

Cikin jawabinsa, Farfesa Amupitan ya jaddada cewa manufarsa ita ce gina tsarin da zai dawo da cikakken amincewar jama’a ga hukumar INEC.

Majalisar Dattawa ta tabbatar Amupitan

An tabbatar da nadin Farfesa Amupitan bayan zaman da Majalisar Dattawa ta yi, inda aka yi masa tambayoyi na tsawon sa'o'i uku.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya tabbatar da amincewar majalisar bayan an kada kuri’ar da ba ta fuskanci wata adawa ba daga ‘yan majalisa.

Kara karanta wannan

Amupitan: Majalisa ta cin ma matsaya kan nadin sabon shugaban INEC da Tinubu ya yi

Shugaban majalisar dattawa
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio. Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Akpabio ya yi kira ga sabon shugaban INEC da ya tabbatar da cewa an yi adalci a dukkan zabubbukan da za su biyo baya.

Shugaban majalisar ya bayyana cewa an riga an tantance Amupitan daga ofishin DSS, mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro (NSA), da Sufeton ‘Yan sanda na kasa (IGP).

'Dan APC ya ce za su murde zabe

A wani rahoton, kun ji cewa wani dan APC a jihar Kano, Garba Kore ya ce za su murde zaben jihar Kano ko da sun fadi.

Garba Kore ya bayyana haka ne bayan tabbatar da cewa jagoran NNPP a Kano, Rabiu Kwankwaso ya fi su jama'a.

Ya yi kira ga Rabiu Kwankwaso, Abba Kabir Yusuf da sauran 'yan NNPP da su koma APC domin karfafa siyasarsu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng