Atiku Ya Tabo Batun Takara a 2027, Ya Fadi Abin da Zai Yiwa Yan Najeriya

Atiku Ya Tabo Batun Takara a 2027, Ya Fadi Abin da Zai Yiwa Yan Najeriya

  • Atiku Abubakar ya nuna alamar zai sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027, yana mai jajjada yaki da cin hanci
  • Ya jaddada cewa ba zai yarda da sata ko cin hanci ba a gwamnatinsa, idan har ya samu mulki a Najeriya
  • Atiku da wasu ‘yan adawa sun kafa kawance karkashin ADC, amma ana ce-ce-ku-ce kan wanda zai samu tikitin shugaban ƙasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya yi magana kan sake tsayawa takara a zaben 2027.

Atiku ya bayyana yiwuwar sake tsayawa takarar shugabancin Najeriya a 2027 yayin da ya karɓi tawagar da tsohon sanata, Idris Abdullahi ya jagoranta.

Atiku ya yi magana kan takara a 2027
Atiku ya fadi abin da zai yiwa yan Najeriya a gwamnatinsa. Hoto: Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

Atiku ya magantu kan takarar shugaban kasa

Hakan na cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X a jiya Asabar 5 ga watan Yulin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya ce dole ne a yaki cin hanci da rashawa inda ya ce ba zai taba barin wadanda suke kwashe dukiyar kasa don biyan bukatar kansu ba.

Ya ce:

“Za mu hukunta duk wanda ya ce zai saci ko aikata rashawa, wallahi za mu yake su, ya isa haka.”

Atiku ya ce Najeriya na da dukiya mai yawa amma rashin kyakkyawan shugabanci ya hana cigaba.

Ya ce sabuwar kawance da suka kulla a jam'iyyar ADC za ta yi aiki don sauya rayuwar 'yan Najeriya.

Atiku da wasu shugabannin adawa sun kafa kawancen adawa karkashin jam’iyyar ADC domin su fitar da Tinubu daga mulki a 2027.

Sun ce za su mayar da hankali kan shugabanci nagari domin tsamo Najeriya daga halin da ta tsinci kanta.

Atiku ya yi alkawarin yakar cin hanci da rashawa
Atiku ya yi magana kan takara da yadda zai yi shugabanci Najeriya. Hoto: Atiku Abubakar.
Asali: Getty Images

An fara ce-ce-ku-ce kan hadakar yan adawa

Sai dai akwai cece-kuce kan wanda zai samu tikitin shugaban ƙasa. Datti Baba-Ahmed ya ce wannan ne babban ƙalubale da ke gaban ADC a yanzu.

Ya ce APC a 2015 ta riga ta daura Muhammadu Buhari a matsayin zababben ɗan takara tun kafin zaɓe. Amma ADC ba ta da wanda aka riga aka amince da shi.

Datti ya ce bai kamata Obi ya zama mataimaki ba, ganin yadda ya samu kuri'u sama da miliyan 10 a 2023. Ya ce ya cancanci tikitin shugaban ƙasa.

A nasa martanin, Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya ce wannan kawance ba komai ba ne illa yunƙurin Atiku na neman tikitin PDP a boye.

Keyamo ya ce suna amfani da Obi ne don samun kuri’unsa amma ba za su ba shi tikitin shugaban ƙasa ba.

An jero masu neman takara a ADC

Kun ji cewa tsohon shugaban jam’iyyar ADC, Ralph Nwosu, ya ce shugabanni bakwai daga kawancen adawa na da sha’awar takarar shugaban kasa a 2027.

Nwosu ya ce mutane na marawa Peter Obi, Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi, Nasir El-Rufai baya kuma za a gudanar da zabe a fili.

Ya bayyana cewa jam’iyyun PDP, APC da LP suna rasa mambobinsu zuwa sabuwar kawance, wadda ke son ceton Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.