Haɗaka: An Faɗi Ƴan Siyasa 7 a ADC da Ke Neman Takara domin Karawa da Tinubu

Haɗaka: An Faɗi Ƴan Siyasa 7 a ADC da Ke Neman Takara domin Karawa da Tinubu

  • Tsohon shugaban jam’iyyar ADC, Ralph Nwosu, ya ce shugabanni bakwai daga kawancen adawa na da sha’awar takarar shugaban kasa a 2027
  • Nwosu ya ce mutane na marawa Peter Obi, Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi, Nasir El-Rufai baya kuma za a gudanar da zabe a fili
  • Ya bayyana cewa jam’iyyun PDP, APC da LP suna rasa mambobinsu zuwa sabuwar kawance, wadda ke son ceton Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban jam'iyyar ADC, Ralph Nwosu, ya yi magana kan yan takara a jam'iyyar.

Nwosu ya bayyana cewa akalla manyan shugabanni bakwai daga kawancen adawa na da sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa.

An fadi jiga-jigan da ke neman takara a ADC
An kira Atiku, Obi cikin ƴan siyasa 7 a ADC da ke neman takara. Hoto: Peter Obi, Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

2027: Jigon ADC ya yi magana kan takara

Rahoton Punch ya ce dukansu sun shirya neman kujerar a 2027 domin fuskantar Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nwosu ya bayyana hakan ne a yayin da ake kara rade-radin cewa wasu daga Arewa a cikin wannan kawance suna marawa Peter Obi don yin wa’adin mulki daya.

Kawancen adawa da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, sun amince da amfani da ADC a matsayin dandalin zabe a 2027.

Nwosu ya ce akwai shugabanni bakwai a cikin kawancen da ake kallon su a matsayin masu iya maye gurbin Tinubu, amma ADC za ta bude kofa ga zabin gaskiya.

Baya ga Obi, ya ce akwai magoya bayan Atiku, Amaechi, El-Rufai, Rauf Aregbesola da Bamidele Ajadi, dan takarar gwamna na ADC a Oyo 2023, da ke goyon bayan kowane jagoransu.

Yan siyasa da ke neman takara a ADC
Tsohon shugaban ADCya fadi masu sha'awar takara a cikinta. Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

Yan takara da ke son kujerar shugaban kasa

Nwosu ya fadi yadda wasu magoya baya suka rarrabu domin yin mubaya'a ga yan takarar da suke ganin sun fi sauran.

Ya ce:

“Muna da 'yancin fadin albarkacin baki, a cikin kawance, kowa na da muhimmanci, kuma wannan ne ke kawo armashi a jam’iyyar da muke ginawa.
“Akwai wasu da ke son Aregbesola ya tsaya. Wasu kuma suna son Dr Ganiyu Bamidele Ajadi ya tsaya, wasu kuma suna goyon bayan Amaechi ko Atiku ya tsaya.
“El-Rufai ma na da nasa shirin. Ko Sule Lamido ma na son tsayawa. Na kasance cikin wannan tattaunawa, na san masu sha’awar tsayawa. Ina fada ne daga cikin gida.
“Tsohuwar ADC ma za ta iya marawa Ajadi baya. Wannan ke nuna cewa zaɓen zai kasance a bude. Wannan shi ne dimokuradiyya."

Ya bayyana cewa a yayin da wannan kawance ke kara karfi, magoya bayan masu neman mulki na ci gaba da shirye-shirye, duk da cewa PDP da APC na cigaba da rasa mambobinsu.

'Gwamnoni 5 na shigowa jam'iyyarmu' - ADC

Kun ji cewa jam’iyyar ADC da ke jagorantar gamayyar ‘yan adawa ta fara shirin jawo gwamnoni kafin zaben 2027.

Wasu shugabannin PDP daga jihohi daban daban sun fice daga jam’iyyar suka koma ADC domin hada kai da gamayyar.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Peter Obi sun amince da ADC a matsayin dandali 'yan adawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.