Bayan Hatsaniya a Gombe, Zulum Ya Feɗe Gaskiya kan Jita Jitar Barin APC Zuwa ADC

Bayan Hatsaniya a Gombe, Zulum Ya Feɗe Gaskiya kan Jita Jitar Barin APC Zuwa ADC

  • Gwamna Babagana Umara Zulum ya yi martani kan jita-jitar komawarsa ADC tare da wasu gwamnoni
  • Zulum ya ƙaryata hakan yana cewa makircin 'yan siyasa ne da ke neman tayar da kura ba tare da hujja ba
  • Ya ce rahoton karya ne daga masu nufin ganin rikici a siyasa, yana mai jaddada cewa biyayyarsa ga jam’iyyar APC ba ta canzawa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya fede gaskiya kan cewa zai koma ADC.

Zulum ya karyata jita-jitar cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar ADC ta haɗaka.

Zulum ya yi magana kan jita-jitar barin APC
Zulum ya musanta rade-radin zai bar APC zuwa ADC. Hoto: @ProfZulum.
Asali: Twitter

Zulum ya yi magana kan barin APC

Zulum ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a yau Lahadi 6 ga watan Yulin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Zulum ya ce rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta ba gaskiya ba ne, yana cewa karya ce daga masu son tada husuma.

Ya bayyana cewa sunan wasu gwamnoni guda biyar ma an hada su a cikin wannan jita-jita, duk kuwa da cewa ba gaskiya ba ne.

Ya ce:

“Wannan jita-jita karya ce tsagwaronta, ni dai ina nan daram a cikin APC kuma ina aiki domin cigaban jihar Borno."
Zulum ya jaddada biyayyarsa ga APC
Zulum ya ƙaryata labarin barin APC zuwa ADC. Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum.
Asali: Facebook

Zulum ya ba yan Borno shawara

Gwamnan ya bukaci mutanen jihar Borno da su yi watsi da jita-jitar, yana mai cewa gwamnati tana kan gaba wajen aikin raya jiha.

Zulum ya kara da cewa bai da lokacin shiga siyasar banza, ya kuma bukaci mutane da su nemi sahihan bayanai daga hukumomi na gaskiya.

Ya ce akwai ayyuka masu nauyi a gaban su na farfado da jihar, don haka bai kamata a dame su da batutuwan da ba su da amfani ba.

A karshe, ya tabbatar da cewa biyayyarsa ga jam’iyyar APC tabbatacciya ce kuma yana nan a shirye don ci gaba da hidima.

Sanarwar ta ce:

"Na samu labarin wani rahoto na bogi da ke yawo a kafafen sada zumunta, inda ake zargin cewa ina shirin ficewa daga APC zuwa ADC tare da wasu gwamnoni guda biyar.
"Wannan zargi ƙarya ne ƙiri-ƙiri, kuma yana cikin tunanin waɗanda suka ƙirƙira shi kawai saboda bukatar kansu.
"Su ne masu neman kawo cikas waɗanda ba su da wata gudunmawa ga cigaban Jihar Borno ko Najeriya.
"Wannan misali ne na yunkurin yaɗa jita-jita marasa tushe, da ke da nufin karkatar da hankali da tayar da hayaniya a siyasa."

Ana zargin Zulum da kai hari kan Ganduje

Mun ba ku labarin cewa wata kungiyar APC daga Arewa ta Tsakiya ta bukaci Gwamna Babagana Zulum ya ba da hakuri kan abin da ya faru a Gombe.

Kungiyar ta zargi Zulum da daukar nauyin'yan daba da suka kai wa Abdullahi Ganduje hari a taron jam'iyyar a jihar Gombe.

Shugaban kungiyar, Zazzaga ya zargi Zulum da kawo rikici a taron APC, ya ce bai dace ya hana shugaban jam'iyya aikinsa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.