'Gaba Ta Kai Mu,' Ministan Tinubu Ya Hango Amfanin da ADC Za Ta Yiwa APC a 2027

'Gaba Ta Kai Mu,' Ministan Tinubu Ya Hango Amfanin da ADC Za Ta Yiwa APC a 2027

  • Wasu daga cikin jagorori a gwamnatin APC sun fara martani ga yunkurin yan adawa na curewa a jam'iyyar ADC
  • A ranar Laraba ne jiga-jigai a siyasar Najeriya suka amince da amfani da ADC a matsayin dandalin adawa da APC
  • A martaninsa, Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo SAN na ganin wannan ba zai yi wa APC illa ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Ministan harkokin jiragen sama, Festus Keyamo ya ce sabon matakin da wasu fitattun ‘yan siyasa suka dauka na shiga ADC ya ƙara wa jam’iyyar APC ƙarfi.

Keyamo yana wannan batu ne yayin da manyan yan APC suka fara sauya sheka zuwa ADC bayan an amince da shiga cikinta don fafatawa da jam'iyya mai mulki.

Festus Keyamo ya yi magana kan ADC
Festus Keyamo ya ce APC za ta mori hadakar adawa Hoto: Festus Keyamo
Asali: Facebook

Ta cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Keyamo ya ce ta tabbata, hadakar ta kashe manyan jam'iyyun adawa da za su iya fada a ji a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin Festus Keyamo kan ADC

Festus Keyamo ya ci gaba da cewa shigar manyan yan siyasa ADC ya ruguza adawa a kasar nan, musamman daga manyan jam'iyyun PDP da LP da ke fada a ji.

Ya ce:

“Abin da ya faru yau (Laraba) da safe game da shigowar gungun ‘yan adawa cikin jam’iyyar ADC shi ne abu mafi ƙarfi da ya ƙarfafa APC gabanin 2027."
Ministan sufurin saman Najeriya, Festus Keyamo
Festus Keyamo ya caccaki yan adawa Hoto: Festus Keyamo
Asali: Twitter

Ya ƙara da cewa tun bayan zaɓen 2023, APC ce ke ci gaba da karɓar ƙarin yan siyasa, daga ciki har da gwamnoni, da yan majalisa, yayin da jam’iyyun adawa ke samun matsala.

Keyamo SAN ya ce:

“Tun bayan zaɓen 2023, APC ce ke ƙara ƙarfi. Idan ka kwatanta waɗanda suka shigo APC da waɗanda suka fita, za ka gane inda karfi ya fi karkata.”

Festus Keyamo ya caccaki yan adawa

Keyamo ya bayyana cewa dokar zaɓe ta hana mutum kasancewa cikin fiye da ɗaya daga cikin jam’iyyun siyasa.

Ya ce don haka fitowar waɗanda suka shiga ADC daga PDP da LP na nuni da sun bar tsofaffin jam’iyyunsu zuwa jam'iyyar hadaka.

Keyamo na ganin sabon haɗin gwiwar da aka ƙaddamar karkashin ADC da David Mark a matsayin shugaban rikon ƙwarya, yunkurin Atiku Abubakar ne na mulkin Najeriya.

“Wannan taro ba komai ba ne illa ɓangaren Atiku na PDP da ke kokarin samo tikitin takarar shugaban ƙasa."

Ministan ya yi zargin cewa waɗanda suka shirya wannan sabuwar haɗakar siyasa na ƙoƙarin amfani da Peter Obi, amma ba su da niyyar ba shi tikitin shugaban ƙasa.

ADC: Jigo a PDP ya sauya sheka

A baya, mun wallafa cewa Ibrahim Ali Amin Little, tsohon ɗan takarar gwamnan Kano kuma jigo a jam’iyyar hamayya ta PDP ya fice daga cikinta saboda rikice-rikicen shugabanci.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa da ya aika zuwa ga shugaban PDP na mazabar Tudun Wada, inda ya ce yanzu lokaci ne na kokarin inganta rayuwar yan Najeriya.

A cikin wasikar, Ali Amin Little ya bayyana takaicinsa a kan yadda jam'iyyar ta gaza shawo matsalolin da suke kokarin wargaza ta a matakin kasa baki daga da jiha.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.