Hanyoyi 7 Masu Sauƙi da Za Ka Shiga Jam'iyyar Haɗaka ADC ko Wata Jam'iyya a Najeriya
Ƴan Najeriya na ci gaba da tattaunawa kan tasirin da sabuwar haɗakar ƴan adawa za ta iya yi a babban zaɓen shugaban kasa mai zuwa a 2027.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Manyan jagororin adawa karkashin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar sun kaddamar da ADC a matsayin jam'iyyar haɗaka.

Asali: Twitter
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa haɗakar da ƴan adawar suka yi a ADC ta lashi takobin kayar da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyarsa ta APC.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi, tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai da wasu jiga-jigai duk sun rungumi wannan haɗaka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shiga Jam’iyyar siyasa a Najeriya
Shiga jam’iyyar siyasa a Najeriya hanya ce mai sauƙi da ke ba ɗan ƙasa damar halartar ayyukan dimokuraɗiyya da koƙarin kawo ci gaba a yakinsa, Tribune Online ta rahoto.
Legit Hausa ta tattaro maku yadda za ku iya shiga sabuwar jam'iyyar haɗaka watau ADC ko wata daga cikkn jam'iyyun siyasa a Najeriya, ga hanyoyin kamar haka:
Abubuwan da ake bukatar mutum ya cika
- Dole ne ka kasance kana da aƙalla shekara 18 ko fiye da haka na haihuwa
- Dole ne ka kasance ɗan asalin ƙasar Najeriya
- Ka cika ƙa’idodin da jam’iyyar da kake sha'awar shiga ta shimfiɗa don zama mamba
Matakan shiga ADC ko wata jam’iyya a Najeriya
1. Zaɓi Jam’iyya: A farko, za ka zaɓi jam’iyyar da ta dace da tunaninka da manufofinka, misali ADC, APC, PDP ko wata jam'iyya.
2. Zuwa ofishin mazaba: Daga nan sai ka je ofishin jam’iyyar da ke matakin mazaba watau gundumarka domin karɓar fam din rijista.
3. Cika fom: Bayan ka karɓa za ka cike haƙiƙanin bayananka da aka nema a jikin wannan fam.
4. Biyan kudin rajista: Daga nan zaka biya kuɗin rijistar da jam'iyyar ta ware idan da buƙatar hakan amma galibin jam'iyyu suna yin rijistar mambobi ne kyauta.
5. Mayar da fam: Za ka koma ofishin mazaɓa ka mayar da fam ɗin da ka karɓo ka cike ga kwamitin gudunarwa na wannan mazaɓa domin tantancewa.
6. Mallakar katin jam'iyya: Idan aka amince da duka bayanan da ka gabatar, za a baka katin zama cikakken mamban wannan jam'iyya tare da hotonka a jiki.
7. Halarta ayyukan jam’iyya: Bayan cika waɗannan sharuɗɗan, kana da damar halartar tarukan jam'iyya tare da bayar da gudummuwa wajen kawo ci gaba.

Asali: Twitter
ADC ta fara zawarcin Gwamna Dauda Lawal
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar ADC reshen jihar Zamfara ta yi kira ga Gwamna Dauda Lawal da ya watsar da PDP, ta shigo haɗakar ƴan adawa.
Shugaban jam’iyyar ADC a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma, Alhaji Kabiru Garba, ya bayyana cewa yana cigaba da karbar masu sauya sheka daga jam'iyyu daban-daban.
Kabiru Garba ya kuma bayyana cewa jam’iyyar ADC a shirye take ta karɓi Gwamna Dauda Lawal idan har ya yanke shawarar sauya sheƙa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng