An Shirya Gangami, Ɗan Majalisar Tarayya, Shugabanni da Ƴan Siyasa 10,000 Sun Koma APC

An Shirya Gangami, Ɗan Majalisar Tarayya, Shugabanni da Ƴan Siyasa 10,000 Sun Koma APC

  • Jam'iyyar LP ta sake gamuwa da koma baya yayin da Ɗan Majalisar Wakilai ya sauya sheƙa zuwa APC a jihar Enugu
  • Hon. Sunday Uneha ya ja ragamar shugabannin LP a mazaɓar Udi/Ezeagu ciki har da tsohon ɗan Majalisa, zuwa jam'iyyar APC
  • Ɗan Majalisar ya ce ya yanke shawarar haɗewa da APC ne domin bai wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu goyon baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Enugu - Guguwar sauya sheƙa ta ƙara turnuƙe jam'iyyun adawa a Najeriya yayin da shirye-shiryen babban zaɓen 2027 ke ƙara kankama a ƙasar nan.

A wannan karon, guguwar ta mamaye jam'iyyar LP reshen jihar Enugu da ke Kudu maso Gabashin Najeriya, inda ta yi awon gaba da shugabanni zuwa APC.

Hon Sunday Umeha ya koma APC.
Hon Sunday Umeha ya sauya sheka daga LP zuwa APC a Enugu Hoto: Hon Sunday Umeha
Asali: Twitter

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ita ce ta samu ƙaɗuwa, yayin da LP ta sake fuskantar tangarɗa da koma ɓaya a jihar Enugu, rahoton AIT Nigeria.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan majalisa da mambobi 10,000 sun shiga APC

Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Udi/Ezeagu, Hon Sunday Umeha tare da manyan ƙusoshin jam'iyyar LP sun sauya sheƙa zuwa APC

Daga cikin jagororin LP da suka koma APC a Enugu har da tsohon ɗan Majalisar wakilai da magoya bayan LP akalla 10,000.

Waɗannan shugabanni da magoya baya sun tabbatar da shiga APC ne a wani gangami na musamman da aka shirya masu a mazaɓar Udi/Ezeagu.

Da yake jawabi ga manema labarai, Hon. Umeha ya bayyana cewa ya koma APC ne ba don komai ba sai don samun damar goyon bayan Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Me yasa suka sauya sheƙa zuwa APC

A cewarsa, gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Tinubu ta ɗauko hanyar gyara Najeriya, don haka tana buƙatar goyon baya daga duka ƴan ƙasa.

Ɗan Majalisar ya yaba da ƙoƙarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen kawo ci gaba a fannin ababen more rayuwa a Jihar Enugu da yankin Kudu Maso Gabas baki daya.

Shugabannin jam’iyyar APC reshen jihar Enugu sun tarbi masu.sauya sheƙar da hannu bibbiyu a wuron taron da aka shorya, rahoton Daily Post.

APC ta ƙara nakasa LP a jihar Enugu.
Shugabanni da mambobi sama da 10,000.na LP sun sauya sheka zuwa APC Hoto: @LabourNG, @OfficialAPCNig
Asali: Twitter

APC ta yi maraba da masu sauya sheƙa a Enugu

Waɗanda suka halarci taron daga cikin manyan APC a Enugu sun haɗa da ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji; mataimakin Shugaban jam’iyya na kasa daga yankin Kudu Maso Gabas, Emma Enukwu.

Shugaban APC na jihar Enugu, Barista Ugo Agballah, na daga cikin waɗanda suka halarci taron tarbar dubannin masu sauya sheka.

Jagororin APC da suka je wurin tarbar sun bayyana yawaitar canza jam’iyyar siyasa matsayin alamar da ke nuna gazawar shugabancin PDP a Jihar Enugu..

Ƴan Majalisa 8 sun sauya sheka a Abuja

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC ta samu ƙarin ƴan Majalisa shida yayin da PDP samu karin mutum biyu a Majalisar Wakilai.

Ƴan Majalisan shida sun bar PDP zuwa APC a hukumance a wasiƙar da suka miƙa kuma kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas karanta a zama. Majalisa.

Ƴan majalisun sun bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da rabuwar kawuna da suka dabaibaye jam’iyyunsu ne suka tilasta musu sauya sheƙa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262