Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamna Fintiri Na Jihar Adamawa

Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamna Fintiri Na Jihar Adamawa

  • Kotun zabe ta kori karar jam'iyya SDP da dan takararta, ta tabbatar da nasarar Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa
  • Sai dai har yanzu Kotun ba ta yanke hukunci kan karar da Aishatu Binani ta jam'iyyar APC ta shigar kan zaben ba
  • Hukumar zabe INEC ta ayyana gwamna Fintiri a matsayin wanda ya samu nasara a zaben ranar 18 ga watan Maris, 2023

Jihar Adamawa - Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Adamawa ta kara tabbatar da nasarar Gwamna Ahmadu Umar Fintiri na jiha Adamawa.

Umar Ardo, dan takarar Social Democratic Party (SDP), da jam’iyyarsa su ne suka kalubalanci nasarar gwamna Fintiri a gaban kotun, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa.
Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamna Fintiri Na Jihar Adamawa Hoto: Ahmadu Fintiri
Asali: Facebook

Dan rakarar da kuma jam'iyyar SDP sun shaida wa Kotu cewa suna zargin an tafka kura-kurai, barazana da tada zaune tsaye lokacin zabe na watan Maris.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotun Zabe Ta Kwace Kujerar Gwamnan APC A Jihar Arewa, Ta Bai Wa PDP

Bisa wadan nan zarge-zarge ne masu shigar da karar suka roki Kotu ta soke zaben gaba daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

UKotu ta yanke hukunci kan wannan kara

Da take yanke hukunci ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba, 2023, shugaban kwamitin alkalan Kotun mai shari'a Theodora Uloho, ta kori karar bisa rashin cancanta.

"Takardar karar ba ta dace ba kuma ba a shigar da ita yadda ya kamata a gaban kotu ba. Masu gabatar da kara ba su da tabbacin abin da suke bukata."inji ta.

Gwamnatin Adamawa ta maida martani

Da take maida martani kan hukuncin kotun, Kaletapwa George-Farauta, mataimakiyar gwamnan Adamawa, ta bayyana hakan a matsayin nasara ga dimokuradiyya.

Ta bukaci masu shigar da kara da su hada hannu da gwamnatin Fintiri domin gina sabuwar jihar Adamawa, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Gwamnan APC ya sha a kotu, an yi watsi da karar dan takarar PDP

Har yanzu kotun ba ta yanke hukunci kan karar da Aisha Binani, ‘yar takarar gwamna a inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta shigar game da zaben ba.

A halin da ake ciki, Sylvester Emmanuel, lauya ga Ardo na SDP, ya ce wanda yake karewa zai daukaka hukuncin zuwa Kotun daukaka kara.

Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani Game da Wanda Kotu Ta Ce Ya Ci.Zaben Nasarawa

A wani rahoton na daban kuma Kotun zaɓe ta bayyana ɗan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe.zaben gwamnan jihar Nasarawa a watan Maris.

Alƙalan Kotun sun sauke gwamna Abdullahi Sule na jam'iyyar APC.daga matsayin gwamna ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel