2027: Kalaman El Rufai kan 'Makomar Tinubu' Sun Tada Ƙura, Minista Ya Maida Martani
- Kalaman tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai na mayar da Bola Tinubu Legas a zaɓen 2027 sun fara jan hankalin jiga-jigan gwamnati
- Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris ya ce Tinubu zai bar mulki ya koma Legas amma bayan ya gama wa'adi na biyu
- Mohammed ya kuma musanta raɗe-raɗin cewa Tinubu zai sauya Shettima a 2027, yana mai cewa zaɓen abokin takara haƙƙin shugaban ƙasa ne
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da kan Al’umma, Mohammed Idris, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai koma jihar Legas ne bayan kammala wa’adi na biyu.
Mohammed Idris ya yi wannan kalamai ne a matsayin martani ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, wanda ya ce za su mayar da Tinubu Legas a 2027.

Asali: Twitter
Ministan ya bayyana haka ne yayin wata hira da ya yi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kwanakin baya, El-Rufa’i ya ce haɗakar jam’iyyun adawa da suke shirin kafawa za ta tura Tinubu ya koma Legas a 2027 a matsayin wanda ya yi ritaya daga shugabanci.
Minista ya mayar da martani ga Nasir El-Rufai
Da yake martani, Mohammed Idris ya ce Shugaba Tinubu yana yin aiki mai kyau a fannoni da dama, yana mai jaddada cewa tattalin arzikin Najeriya na farfaɗowa.
“Eh, Shugaban Ƙasa zai koma Legas a ƙarshe, da yardar Allah, amma sai bayan kammala wa’adinsa na biyu, muna sa ran zai koma Legas.
"Duka waɗannan abubuwan alherin da kuke gani, shekara biyu kacal ya yi a kan madafun iko. Lokacin da Tinubu ya hau mulki, gwamnatinsa ta ɗauki muhimman matakai biyu.
"Na farko, daidaita tsarin musayar kudi, na biyu kuma cire tallafin fetur. Wadannan matsaloli ne da suka dade suna damun ƙasarmu.”
- Mohammed Idris.
Shugaba Bola Tinubu ya fara gyara Najeriya
Ya ƙara da cewa duk da ba za su tabbatar da cewa an share duka hawayen Najeriya ba, amma shugaban ƙasa ya kawo ci gaba a fannoni daban-daban, Daily Trust ta rahoto.
"Ba za mu ce an warware komai ba amma gwamnati na tafiya kan turba mai kyau. Tattalin arziki yana farfaɗowa, al’amura na kyautatuwa, farashin abinci ba kamar bara, tsadar ta ragu," in ji shi.

Asali: Twitter
Bola Tinubu na shirin sauya Shettima a 2027?
Ministan ya kuma karyata jita-jitar cewa Shugaba Tinubu yana shirin sauya mataimakinsa, Kashim Shettima, a zaɓen shekarar 2027.
Mohammed Idris ya nanata cewa zabin abokin takara haƙƙin shugaban ƙasa ne shi kaɗai, babu wanda zai yi masa katsalandan.
“Wannan kawai a tunanin wasu mutane ne, shugaban ƙasa da mataimakinsa suna aiki tare sosai, siyasa ce kawai.
"A lokacin da aka ba Tinubu tikitin takara a 2023, ka ji sunan Shettima? Shi ne ya zaɓe shi. Zaɓin wa zai zama mataimaki hakkin shugaban ƙasa ne," in ji shi.
SDP ta hango faɗuwar Tinubu a 2027
A wani labarin, kun ji cewa shugaban SDP a jihar Ebonyi, Dr Kingsley Agbor ya yi ikirarin cewa APC ta sha ƙasa a zaɓen 2027 kamar yadda ake kifar da PDP a 2015.
Ya ce matsin rayuwa ya karya yardar da mutane suka yi wa APC kuma a yanzu sun ƙosa zabe ya zo su sauke fushinsu ta hanyar amfani da kuri'a.
Kingsley Agbor, ya kuma bayyana cewa jam’iyyarsu ta SDP na ci gaba da kara karfi da yaɗuwa a faɗin ƙasar nan domin fuskantar APC a 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng