Hamza Al Mustapha Zai Fito Takarar Shugaban kasa a 2027, Ya Tsayar da Jam'iyya

Hamza Al Mustapha Zai Fito Takarar Shugaban kasa a 2027, Ya Tsayar da Jam'iyya

  • Manjo Hamza Al-Mustapha, tsohon dogarin Sani Abacha, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027 a ƙarƙashin SDP
  • Ya bayyana wannan kuduri a Minna, inda ya jaddada aniyar sa ta yi wa Najeriya hidima da dawo da martabarta idan ya samu shugabanci
  • Shugaban SDP na Neja, Buhari Yakubu Yarima, ya yi maraba da kudurin Al-Mustapha, yana mai fatan jam'iyyar za ta karbi mulki a 2027

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - Tsohon babban dogarin tsohon shugaban Najeriya, Janar Sani Abacha, watau Manjo Hamza Al-Mustapha zai tsaya takarar shugaban kasa a 2027.

A hukumance, Manjo Hamza Al-Mustapha ya bayyana shirinsa na neman mulkin Najeriya a babban zaben 2027 a karkashin jam'iyyar SDP.

Manjo Hamza Al-Mustapha ya bayyana kudurinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2027
Tsohon babban dogarin Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha. Hoto: Shehu Musa Gabam
Asali: Facebook

Al-Mustapha zai tsaya takara a 2027

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya ya sanar da kudirinsa ne a Minna, babban birnin jihar Neja a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya nuna cewa tsohon dogarin na Abacha ya shaida wa kwamitin gudanarwar jam'iyyar SDP na jihar da magoya bayansa wannan kuduri nasa a taron da suka yi.

Yayin da yake jawabi a wajen taron, Manjo Hamza Al-Mustapha ya jaddada kudurinsa na yi wa Najeriya hidima da kuma dawo da martabarta a idon duniya.

A cewarsa:

"Na damu matuka da halin da Najeriya ke ciki yanzu. Sai dai duk da cewa, idan har aka samu shugabanci na-gari, to kasar za ta dawo da martabarta.
"Duk da cewa hanyar da muka dauka za ta iya zama mai cike da tudu da gangara, amma idan muka yi aiki tare, to za mu sake gina Najeriya."

"Na gama shirin tunkarar 2027" - Al-Mustapha

Ya bayyana wannan taro a matsayin daya daga cikin tsare-tsarensa na tattunawa da masu ruwa da tsaki a fadin kasar nan, yayin da yake shirin tunkarar zabukan 2027.

A cewar wata sanarwa da Jubril Umar Sanda, daraktan wata labarai na yakin neman zaben tsohon dogarin Abacha, Hamza Al-Mustapha ya ce:

"Na riga da na kammala duk wani shiri na tunkarar wannan kudiri, na shirya yin jagoranci bisa gaskiya, jarumtaka da kuma tsare-tsare na kawo ci gaba."

Manjo Hamza Al-Mustapha, wanda ya tsaya a Minna a hanyarsa ta zuwa Mokwa domin jajanta wa wadanda ambaliya ta shafa, ya nuna buakatar samar da hadin kai, da shugabannin da za su kawo karshen matsalolin Najeriya.

Manjo Hamza Al-Mustapha ya ce kammala shirin tsayawa takara kuma zai yi shugabanci bisa adalci
Tsohon babban dogarin Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha. Hoto: Dr. Hamza Al-Mustapha
Asali: Facebook

SDP ta yi maraba da kudurin Al-Mustapha

Shugaban jam'iyyar SDP na jihar Neja, Alhaji Buhari Yakubu Yarima, ya yi maraba da kudurin Al-Mustapha tare da jinjina masa kan burinsa na ci gaban kasa.

Ya kuma nuna yakininsa kan babbar rawar da jam'iyyar za ta taka a babban zaben 2027 da ke tafe, yana mai cewa:

"Muna da yakinin cewa idan muka samu 'yan takarar da suka cancanta, kuma suke da burin ci gaban kasa, to SDP za ta karbi mulki a Najeriya a 2027."

- Alhaji Buhari Yakubu.

Hamza Al-Mustapha ya shiga sahun manyan 'yan siyasa da suka fito suka bayyana kudurinsu na neman shugabancin Najeriya, yayin da kasar ke hannun Shugaba Bola Tinubu yanzu.

Hamza Al-Mustapha ya sauya sheka zuwa SDP

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP a Abuja, lamarin da ya jawo hankalin jama'a, kan rawar da zai taka a 2027.

Shugaban jam’iyyar SDP na ƙasa, Shehu Musa Gabam, ya bayyana cewa wannan sauyi ne mai muhimmanci a siyasar Najeriya.

Shehu Musa Gabam ya kuma nuna kwarin gwiwa cewa zuwan Al-Mustapha zai kawo sabon salo da kuma ƙarfafa jam'iyyar a dukkanin matakai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.