Al Mustapha Ya Fadi yadda aka Samu Gawar Abacha bayan Mutuwar Shi a Aso Villa

Al Mustapha Ya Fadi yadda aka Samu Gawar Abacha bayan Mutuwar Shi a Aso Villa

  • Tsohon dogarin Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Almustapha, ya bayyana cewa mutuwar shugaban da MKO Abiola ta faru ne ta hanyar iri ɗaya
  • Almustapha ya ce batun rushe zaɓen 12 ga Yuni 1993 ya fi yadda mutane ke fahimta girma, kuma ya ce ba yanzu zai fadi gaskiyar abin da ya faru ba
  • Ya kuma nesanta kansa daga zargin da Janar Ibrahim Babangida ya yi wa Abacha a littafinsa game da rushe zaɓen 1993 da aka ce Abiola ya lashe

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A yau ake bikin ranar Dimokuraɗiyya a Najeriya, wanda ake tunawa da zaɓen da aka soke na 12 ga watan Yuni 1993.

Tsohon dogarin shugaban kasa na mulkin soja, Manjo Hamza Almustapha, ya yi wasu muhimman bayanai.

Al Mustapha ya yi magana kan mutuwar Abacha
Al-Mustapha ya ce Abacha ya yi irin mutuwar Abiola. Hoto: Hamza Al-Mustapha|Getty Images
Asali: Facebook

Manjo Hamza Al-Mustapha ya yi magana kan wasu abubuwa da suka faru ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Almustapha da ya kasance babban dogari ga Janar Sani Abacha, ya ce akwai abubuwa masu zurfi da mutane ba su sani ba game da zaɓen da aka soke da kuma mutuwar MKO Abiola.

Tsohon dogarin ya nesanta kansa daga batutuwan da suka shafi littafin Ibrahim Babangida, da kuma bayyana irin yadda tsohon maigidansa da Abiola suka mutu.

'Mutuwar Abacha da Abiola iri daya ce' – Almustapha

Legit ta rahoto cewa a lokacin da aka tambayi Hamza Al-Mustapha game da mutuwar Janar Abacha, ya ce:

“Wannan wata magana ce babba da na yi bayani a gaban Oputa Panel. Yadda Abiola ya mutu, haka Abacha ma ya mutu. Zuciyarsu ce ta kumbura fiye da yadda ake tunani.”

Wannan bayani ya sake tayar da tambayoyi a zukatan jama’a kan yuwuwar an yi wani abu da bai dace ba kan wadannan manyan mutane biyu da mutuwarsu ke da tasiri sosai a tarihin Najeriya.

An dade ana zargin cewa akwai wani abu da ya buya game da mutuwar su, musamman ganin cewa duk sun rasu ne a cikin wani yanayi da ba a fayyace ba.

Maganar Almustapha kan Janar Ibrahim Babangida

A littafinsa da ya wallafa, tsohon shugaban mulkin soja Janar Ibrahim Babangida ya ce ya yi nadama kan rushe zaɓen 12 ga Yuni.

Baya ga haka, Janar Babangida ya kuma ɗaura laifin a kan Janar Abacha, wanda ya ce ya yi katsalandan.

Al Mustapha ya musa zargin IBB
Al Mustapha ya ce zai yi magana kan rusa zaben Abiola a gaba. Hoto: Hamza Al-Mustapha
Asali: Facebook

Sai dai da aka tambayi Almustapha game da wannan zargi, ya ce:

“Lokacin da aka ƙaddamar da littafin ba a gayyace ni ba. Kuma ban karanta littafin ba, don haka ba zan ce komai yanzu ba.”

Ya kara da cewa:

“Batun 12 ga watan Yuni ya fi ƙarfin yadda jama’a ke tunani, saboda abin da ya faru a wancan lokacin jama’a ba su sani ba. Ni kuma ba yanzu zan fadi abin da ya faru ba.”

Hamza Al-Mustapha ya koma jam'iyyar SDP

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon dogarin Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya sauya sheka zuwa SDP.

Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya ya bayyana haka ne yayin da ya ziyarci ofishin jam'iyyar SDP a birnin tarayya Abuja.

Duk da cewa ya yi takarar shugaban kasa a baya, ba a da tabbacin ko zai nemi takara a jam'iyyar ko zai mara wa wani baya a zaben 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng