Hadari: Ministan Buhari, Abubakar Malami Ya Tausayawa Halin da Adam Zango Ya Shiga

Hadari: Ministan Buhari, Abubakar Malami Ya Tausayawa Halin da Adam Zango Ya Shiga

  • Tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya nuna damuwa da addu’a bayan hadarin da Adam A. Zango ya yi a hanyar Kaduna-Kano
  • Ya bayyana hakan ne bayan gama aikin Hajji a kasar Saudiyya, yana mai addu’ar samun sauki da kariya ga fitaccen dan wasan fim din
  • Malami SAN ya jaddada goyon bayansa ga Zango da iyalansa, yana mai cewa suna cikin addu'o'insa a wannan lokaci na jarrabawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kebbi - Tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya bayyana alhininsa tare da mika sakon jaje da addu’a ga shahararren jarumin Kannywood, Adam A. Zango.

Hakan na zuwa ne bayan Adam A. Zango da wasu 'yan fim na Kannywood sun yi hadarin mota a kwanakin baya.

Abubakar Malami ya yi wa Adam Zango addu'a
Abubakar Malami ya yi wa Adam Zango addu'a bayan hadari. Hoto: Abubakar Malami SAN
Asali: Facebook

Legit ta gano sakon jajen da Abubakar Malami SAN ya fitar ne a wani sako da aka wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A sanarwa ya fitar a ranar Talata, 17 ga Yuni, 2025, Malami ya ce ya samu labarin hadarin ne yayin da yake a Saudiyya don gudanar da aikin Hajji.

Addu'ar Abubalar Malami ga Adam A Zango

Sanarwar ta ce Malami na addu’ar Allah ya ba Adam Zango lafiya da sauki cikin gaggawa, tare da ci gaba da kare shi daga dukkan sharri da hatsari.

Malami ya bayyana cewa:

“Na samu labarin hadarin motar da Adam A. Zango ya yi a hanyar Kaduna-Kano.
"A matsayina na wanda ke cikin ibada a Saudiyya, na dauki lokaci na musamman wajen yin addu’a gare shi bayan dawowa ta.”

Ya ce jarumin na da muhimmiyar rawa da ya taka wajen bunkasa fina-finan Hausa da nishadantarwa a Najeriya, wanda hakan ya sa ya cancanci addu’a da goyon baya.

Lauyan ya kara da cewa bayan dawowarsa daga Hajji, yana jin yana da kyau ya fitar da sanarwa don nuna goyon bayansa a hukumance.

Malami ya yaba da gudummawar Adam Zango

Tsohon ministan shari'an kasar ya yaba da gudumawar da Adam A Zango ke bayarwa a harkokin finaninai a Najeriya.

A cewar Malami:

“Adam A. Zango ya taka rawa sosai a ci gaban masana’antar Kannywood ta fuskoki da dama – daga waka zuwa fim – wanda hakan ke daukar hankali”
Abubakar Malami yana hira da 'yan jarida a wani taro
Malami yana hira da 'yan jarida a wani taro. Hoto: Abubakar Malami SAN
Asali: Facebook

Malami ya jaddada goyon baya ga Zango

Malami ya bayyana cewa yana tare da Adam Zango da iyalansa a wannan lokaci na jarrabawa, yana masu fatan samun sauki cikin gaggawa.

“Ku tabbata cewa muna tare da ku da iyalanku gaba daya."

Inji sanarwar da mai taimaka masa kan harkokin watsa labarai, Mohammed Bello Doka, ya sanya wa hannu.

Adam Zango ya yi wa malamin Izala raddi

A wani rahoton, kun ji cewa Adam A Zango ya yi wa malamin Izala, Sheikh Salihu Musa Alburhan raddi.

Sheikh Musa Alburhan ya yi wani wa'azi ne da ya shafi yin waka da sanya alkyabba da hakan ya dauki hankalin mawakin.

Duk da cewa Adam A Zango bai yi wata magana a bidiyon da ya fitar ba, ya nuna alamun cewa yana da ja a kan maganar da malamin ya yi ta hanyar rawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng