Zaben Abuja: Yan takarar kujeran Ciyaman 55, Kansila 363 da zasu kara yau

Zaben Abuja: Yan takarar kujeran Ciyaman 55, Kansila 363 da zasu kara yau

Akalla masu neman kujeran shugabannin kananan hukumomi 55 da masu neman kujerar Kansila 363 yayinda mutum milyan 1.4 zasu musharaka a zaben birnin tarayya Abuja yau Asabar.

Hukumar zaben Najeriya INEC ce zata gudanar da zaben kananan hukumomi shida da kujerun kansiloli 62.

Diraktar cibiyar bibiyar zaben CTA, . Faith Nwadishi, a hira da manema labarai ranar Juma'a a Abuja ta bayyana cewa INEC ta ce jam'iyyun siyasa 14 zasu yi musharaka a zaben.

Ta jinjinawa hukumar zaben bisa namijin shirin da ta yiwa zaben na raba kayayyakin zabe.

Tace:

"Za'a gudanar da zaben Abuja a dukkan runfunana zaben kananan hukumomi shida don mamaye kujeru 68; shida na ciyamomi, 62 na Kansiloli.
"A zaben, mutum 55 na neman kujerun Ciyaman, yayinda mutum 363 ke neman kujerun Kansiloli. Adadin mutanen da sukayi rijistan zabe shine 1,373,492 ."

Kara karanta wannan

Mu hada kai don Tinubu ya zama Shugaban kasa, Gwamna Sanwo-Olu ga shugabannin APC

Zaben Abuja: Yan takarar kujeran Ciyaman 55, Kansila 363 da zasu kara yau
Zaben Abuja: Yan takarar kujeran Ciyaman 55, Kansila 363 da zasu kara yau

Hukumar yan sanda ta bayyana cewa akwai wasu unguwanni 13 da aka tsaurara tsaro sabon yiwuwan barkewar rikici.

Unguwannin sun hada da Karshi, Deidei, Zuma Rock, Kabusa, Gishiri, Abaji Nebu, Yangoji, Yaba, Kwali Kwaita, Mate, Azam, Kuje Pegi da Bwari

Ka jerin yan takaran:

Asali: Legit.ng

Online view pixel