Gwamnonin Arewa 5, Shugabanni APC Sun Amince da Tazarcen Tinubu a 2027

Gwamnonin Arewa 5, Shugabanni APC Sun Amince da Tazarcen Tinubu a 2027

  • Shugabannin APC daga yankin Arewa ta Tsakiya sun amince a marawa Shugaba Bola Tinubu baya domin tsayawa takara a 2027
  • Taron ya gudana ne a Abuja, inda aka bayyana goyon baya bisa shugabanci nagari da Bola Tinubu ke aiwatarwa a Najeriya
  • Jiga-jigan jam’iyyar daga jihohi shida na yankin sun yaba da kafa Hukumar Cigaban Arewa ta Tsakiya da gyaran tsarin tsaron daji

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugabannin jam’iyyar APC daga yankin Arewa ta Tsakiya sun amince da goyon bayan Bola Ahmed Tinubu domin sake tsayawa takara a wa’adin mulki na biyu a 2027.

Matsayar ta biyo bayan wani kudiri da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya gabatar, wanda Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya mara wa baya.

APC Arewa
APC a Arewa ta tsakiya ta amince da tazarcen Tinubu. Hoto: Balogi Ibrahim
Asali: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan Neja, Balogi Ibrahim ya wallafa a Facebook cewa hakan ta faru ne yayin wani taro na shugabannin APC daga yankin da aka gudanar a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin taron, mahalarta sun kuma kada kuri’ar yarda da shugabancin Tinubu, inda suka ce ya kawo sauye-sauye masu ma’ana musamman a yankin Arewa ta Tsakiya da kasa baki daya.

'Yan APC sun yaba da nasarorin Bola Tinubu

Gwamnan Nasarawa kuma shugaban kungiyar gwamnonin Arewa ta Tsakiya, Abdullahi Sule ne ya bayyana matsayin yankin game da Tinubu.

Gwamna Abdullahi Sule ya ce gwamnonin sun yi alkawarin ci gaba da kawo zaman lafiya da gina yankin.

Shugabannin da suka fito daga jihohi shida na yankin – Neja, Nasarawa, Kogi, Kwara, Filato da Benue – sun yaba da ayyukan da Tinubu ke aiwatarwa da suka shafi rayuwar jama’a kai tsaye.

Daga cikin abubuwan da suka janyo yabo akwai kafa Hukumar Cigaban Arewa ta Tsakiya da kuma shirye-shiryen kafa rundunar tsaron gandun daji domin yaki da matsalar rashin tsaro.

Ganduje ya ce manufofin Tinubu na aiki

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa manufofin da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa sun fara haifar da da mai ido a fadin kasar.

A kan haka ya bukaci 'yan Najeriya su cigaba da mara baya ga gwamnatin shugaba Bola Tinubu domin karasa ayyukan da ya fara.

Ganduje
Ganduje ya yaba da kokarin Tinubu. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

Taron ya samu halartar gwamnonin Arewa ta Tsakiya, tsofaffin gwamnoni da mataimakansu, ministoci masu ci da wadanda suka gabata.

Haka zalika’yan majalisa na yanzu da na baya, da sauran jiga-jigan jam’iyyar APC daga yankin sun halarci taron.

An ce taron na cikin matakan tabbatar da zaman lafiya, dorewar mulki da kuma inganta dimokuraɗiyyar Najeriya.

ADC za ta yi taron kan yi wa Tinubu hadaka

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar ADC za ta gudanar da muhimmin taro a Abuja domin yanke matsaya kan yi wa Bola Tinubu taron dangi.

Hakan na zuwa ne bayan samun bayanai da suka nuna cewa wasu manyan 'yan adawa sun zabi hada kai a ADC.

Shugaban ADC na kasa ya ce sun shafe sama da wata shida suna tattaunawa kuma bayan taron za su fitar da matsaya kan maganar hadaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng