2027: Shugaba Tinubu Ya Jijjiga Mahaifar Atiku, Dubban Mutane Sun Mamaye Birnin Yola
- Dubban magoya bayan APC sun yi gangami a Yola, jihar Adamawa domin nuna goyon baya ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu
- Ƴan APC sun yi tattaki cikin farin ciki, suna raye-raye da rera waƙa tare da kira ga shugaban ƙasa ya nemi zango na biyu a babban zaɓen 2027
- Shugabannin APC a jihar Adamawa sun halarci gangamin tare da karbar wasu manyan ƴan siyasa da suka sauya sheƙa zuwa jam'iyya mai mulkin Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Yola, jihar Adamawa - Dubban mambobin jam’iyyar APC daga faɗin ƙananan hukumomin jihar Adamawa sun yi gangami a birnin Yola a ranar Alhamis.
Magoya bayan APC sun mamaye titunan Yola ne domin nuna goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da neman ya sake tsayawa takara a zaben 2027.

Asali: Facebook
The Nation ta rahoto cewa waɗanda suka halarci gangamin sun fito ne daga dukkanin ƙananan hukumomi 21 na jihar Adamawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan APC sun yi gangami a birnin Yola
Dubban ƴan APC sun yi dandazo cikin farin ciki da raye-raye tare da rera wakokin goyon bayan Tinubu yayin tattaki daga Gadar Unity Bridge da ke Jimeta zuwa Muna Hotel a Dougirei.
Bayan kammala gangamin, an gudanar da taron manyan jiga-jigan jam’iyyar APC tare da ƙarɓar masu sauya sheƙa daga wasu jam’iyyu zuwa APC.
Daga cikin jiga-jigan da suka sauya sheƙa zuwa APC a taron akwai, tsohon mataimakin gwamna, Crowther Seth, da wani fitaccen ɗan kasuwa, Abdulrahman Haske.
Shugaba Tinubu ya jijjiga mahaifar Atiku
Tsohon Babban Alkalin jihar Adamawa, Ambrose Mamman da tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Gibson Nathaniel na cikin waɗanda suka shiga APC, cewar rahoton Daily Post.
Mataimakin Shugaban APC na Arewa Maso Gabas, Mustapha Salihu, ya ce taron an shirya shi ne don godiya ga Tinubu bisa nasarorin da ya samu cikin shekaru biyu.
Shugabannin APC sun nuna goyon baya ga Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, bisa yadda yake kokarin dakile matsalar tsaro da farfaɗo da martabar Najeriya a idon duniya.

Asali: Facebook
Wasu daga cikin wadanda suka yi jawabi a taron sun haɗa da, tsohon Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, shugaban APC na Adamawa, Barista Shuaibu Idris, da tsohon gwamna Bala James Nggilari.
Dukkansu sun yabawa jagorancin Tinubu, suna masu cewa nan ba da jimawa wahalhalun da manufofi shugaban ƙasa suka kawo, za su wuce tamkar ba a yi ba.
An fara shirin tarawa Tinubu kuri'u miliyan 10
A wani rahoton, kun ji cewa wata kungiyar masu goyon bayan Bola Tinubu , ta bayyana cewa za ta fara kamfen na kasa baki daya domin tara kuri'u miliyan 10 a 2027.
Shugaban rikon kwarya na kungiyar, Sunday Adekanbi ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya kafa tubalin ci gaba mai dorewa a ƙasar nan daga hawansu mulki zuwa yau.
Sunday ya ƙara da cewa manufar Shugaba Tinubu ta samo asali ne daga nasarorin da ya samu lokacin da ya ke gwamnan Jihar Legas da kuma matakan da ya ke dauka a yanzu.
Asali: Legit.ng