Bayan Shan Suka, Wike Ya Yi Martani kan Sanya Sunan Tinubu a Cibiyar ICC

Bayan Shan Suka, Wike Ya Yi Martani kan Sanya Sunan Tinubu a Cibiyar ICC

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan sanya sanya cibiyar ICC sunan Shugaba Bola Tinubu
  • Wike ya bayyana cewa ko kaɗan bai da wata nadama kan matakin da ya ɗauka na sauyawa cibiyar taron ta ƙasa da ƙasa da ke Abuja suna
  • Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya kuma kare maƙudan kuɗaɗen ɗa aka kashe wajen yin gyaran cibiyar taron ta ICC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi martani kan masu sukar sanyawa cibiyar ICC sunan Shugaba Bola Tinubu.

Nyesom Wike ya ce bai yi nadamar sanyawa cibiyar taro ta ƙasa da ƙasa da ke Abuja sunan Shugaba Bola Tinubu ba.

Wike ya tabo batun sanya sunan Tinubu a cibiyar ICC
Wike ya soki masu sukar sanya sunan Tinubu a cibiyar ICC Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Wike ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Juma’a, yayin ƙaddamar da kammala aikin hanyar gefen hagu mai tsawon kilomita 15 daga Ring Road I zuwa kwanar Wassa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu ƴan Najeriya dai sun caccaki sanya sunan Tinubu a cibiyar taron da ke Abuja wadda aka gyara, jim kaɗan bayan sake buɗeta a ranar Talata.

Wasu kuma sun bayyana kashe Naira biliyan 39 wajen gyaran ginin a matsayin abin da bai kamata ba.

Me Wike ya ce kan sanya sunan Tinubu a ICC?

Da yake mayar da martani, Wike ya yi mamakin yadda wasu ke sukar sanya sunan Tinubu a cibiyar.

A cewarsa, filin jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe ba Azikiwe ne ya gina shi ba, haka ma filin wasanni na Moshood Abiola ba Abiola ne ya gina shi ba, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

Ya ƙara da cewa waɗanda ke sukar gyaran cibiyar ba su da kyakkyawan ɗanɗano wajen gane abu mai kyau.

“Na yi abin da ya dace, kuma ban yi nadama ko kaɗan ba."

- Nyesom Wike

Ya bayyana cewa abu ɗaya tilo da bai canza ba a cibiyar shi ne ginin, yana mai cewa komai a cikin cibiyar an sauya shi.

Ya nuna takaicin cewa maimakon su yaba wa Tinubu bisa kyakkyawan abin da ya yi, wasu mutane suna jin daɗi wajen yin sukar da ba ta da tushe.

Wike ya sanya sunan Tinubu a ICC
Wike ya kare kansa kan kudaden da aka kashe wajen gyaran cibiyar ICC Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Nyesom Wike ya kare kashe N39bn

Wike ya ce waɗanda ke cewa kashe Naira biliyan 39 wajen gyaran cibiyar ba shi da muhimmanci, sun manta da yadda abubuwa suka sauya da sauyin darajar Naira da Dala.

"Sun ce an gina cibiyar da Naira miliyan 240, amma a wace shekara? 1991."
"To menene darajar canjin kuɗaɗe a shekarar 1991 idan aka kwatanta da yau? Ku duba fa, 1991 aka gina ta, yanzu kuma muna cikin 2025."
"Babu wanda ke ƙaunar wannan ƙasa da zai soki gyaran cibiyar taron ƙasa da ƙasa."

- Nyesom Wike

Shugaba Tinubu ya ba Wike shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ba da shawara ga ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Shugaba Tinubu ya buƙaci ministan da ya toshe kan masu suka da masu yin ƙananan maganganu kan ayyukan da yake yi a Abuja.

Mai girma Bola Tinubu ya kuma buƙaci Wike da ya maida hankali wajen ci gaba da yin ayyuka masu muhimmanci a birnin Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng