Za a bi Gida Gida Nemawa Tinubu Kuri'a Miliyan 10 a Siyasar 2027
- Wata kungiyar siyasa ta ce za ta hada kuri’u miliyan 10 domin tallafa wa sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027
- Kungiyar da ke karkashin jagorancin dan Neja Delta da aka fi sani da Tompolo za ta yi kiran goyon bayan Shugaba Tinubu gida-gida
- Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan kungiyar sun ce manufofin Bola Tinubu sun daura Najeriya kan turbar ci gaba da hadin kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Wata kungiya da ke goyon bayan Bola Tinubu, ta bayyana cewa za ta fara kamfen na kasa baki daya domin karfafa masa gwiwa da kuma tabbatar da samun nasara a zaben 2027.
Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da maganar zaben 2027 duk da cewa Bola Tinubu ya hana fara masa kamfen a yanzu.

Asali: Twitter
Leadership ta wallafa cewa shugaban rikon kwarya na kungiyar, Sunday Adekanbi ne ya sanar da hakan a Abuja yayin bikin Ranar Dimokuradiyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sunday Adekanbi ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya kafa tubalin ci gaba mai dorewa tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023.
Za a yi wa Tinubu kamfen gida-gida a 2027
Kwamared Adekanbi ya ce kungiyar, wadda ke karkashin jagorancin mai fada aji na yankin Neja Delta da aka fi sani da Tompolo za ta tura wakilanta zuwa kowane lungu da sako na Najeriya .
Kungiyar ta bayyana cewa za ta tura mutanen ne domin wayar da kan al’umma kan ayyukan da gwamnatin Tinubu ke yi.
Tribune ta wallafa cewa Adekanbi ya ce:
“Mun kuduri aniyar ziyartar gidaje da unguwanni a fadin kasar nan domin yada manufofin Tinubu da kuma tabbatar da cewa jama’a sun fahimci nagartattun sauye-sauyen da ake yi,” .
Ya kara da cewa:
“Jagorancin Tompolo zai karfafa hadin kai a tsakanin al’ummomin Najeriya, tare da jaddada sahihancin abubuwan da ake zargi da su game da gwamnatin.
"Zai ziyarci shugabannin gargajiya, ‘yan siyasa da jama’a kai tsaye domin kara musu haske.”
Za a samawa Tinubu kuri'a miliyan 10
Kungiyar ta bayyana cewa manufar Shugaba Tinubu ta samo asali ne daga nasarorin da ya samu lokacin da ya ke gwamnan Jihar Legas da kuma matakan da ya ke dauka a yanzu.
Adekanbi ya ce:
“Sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ya ke aiwatarwa na nuni da jajircewarsa wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da yankin da suka fito ko addininsu ba,”
Kungiyar ta kuma jaddada cewa za ta hada sama da kuri’u miliyan 10 kafin lokacin zabe ta hanyar tuntuɓar jama’a kai tsaye, da kuma nuna musu muhimmancin ci gaba da mulkin Tinubu.
An ce Tompolo zai jagoranci gangamin yakin neman zaben 2027, wanda zai mayar da hankali wajen nuna nasarorin Tinubu da kawar da jita-jitar da ake yadawa game da sauye-sauyensa.

Asali: Facebook
'Yan adawa sun gargadi Tinubu kan 2027
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan adawa sun yi rubdugu wa shugaba Bola Tinubu kan zaben shekarar 2027.
Babban abokin hamayyar Bola Tinubu, Atiku Abubakar ya ce shugaban kasar ya lalata dimokuradiyyar da aka gina a Najeriya.
A daya bangaren, jam'iyyun PDP, ADC da SDP sun ce suna shirye shiryen kwace mulki a hannun Bola Tinubu a zabe mai zuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng