Benue: 'Yan Bindiga Sun Shiga Gida Gida da tsakar Dare, Sun Yi Wa Bayin Allah Kisan Gilla
- Miyagu sun sake kai hare-hare ɗauke da mugayen makamai kan jama'a a yankunan Makurɗi da Katsina-Ala na jihar Benuwai
- Rahotanni sun nuna cewa akalla mutane 26 ne suka rasa rayukansu a hare-haren tsakar dare da ƴan ta'addan suka kai ranar Alhamis
- Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da cewa ta tura dakaru zuwa yankunan da lamarin ya faru domin dawo da zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - Rahotanni sun tabbatar da cewa akalla mutane 26 sun rasa rayukansu sakamakon wasu hare-hare da aka kai cikin dare a jihar Benuwai.
Maharan sun tafka wannan ɓarna ne yayin da suka kai wasu mugayen hare-hare a yankunan kananan hukumomin Makurɗi da Katsina-Ala cikin dare.

Asali: Original
Yadda ƴan bindiga suka kashe rayuka 26
Majiyoyi sun ce ƴan ta'addan sun yi wa mutane 25 kisan gilla a Mtswenem da Akondotyough Bawa da ke yankin North Bank a Makurdi, rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka nan kuma, mutum ɗaya ya rasa ransa a wani harin daban da aka kai Kenvanger da Agbami a gundumar Mbatyula ta karamar hukumar Katsina-Ala.
Wasu mazauna yankin sun ce maharan sun shiga gidaje tsakanin ƙarfe 12 na dare zuwa 2 na safe a ranar Alhamis, dauke da makamai masu haɗari, bindigogi da adda.
Wani ganau mai suna Iorpuu ya bayyana cewa wadanda aka kashe sun haɗa da mata da yara, kuma har yanzu wasu ba a gansu ba.
“Sun shigo ba zato suka fara kashe mutane. Wasu daga cikinmu sun tsere, amma da yawa sun hallaka. Na ji an ce yawan gawarwakin ya ƙaru zuwa 25 domin wasu sun mutu a kan hanyar zuwa asibiti,” in ji shi.
Ƴan bindiga sun tafka ɓarna a kusa da jami'a
Wani shaidar gani da ido da ya nemi a sakaya sunansa ya ce maharan sun kai hari kusa da Jami’ar Noma ta Makurdi, inda suka kashe mutane hudu a farko.
A cewarsa, daga nan suka wuce zuwa wani yanki kusa da Low Cost Housing Estate, inda suka kara kai hari kuma yawan waɗanda suka mutu ya nunka.
A Katsina-Ala, maharan sun shiga Kenvanger da Agbami da misalin ƙarfe 1 na dare, suka yi ƙoƙarin yi wa wasu mata masu shayarwa fyade.
Sai dai kururuwar neman taimako da matan suka yi ya sa wasu maza suka kawo ɗauki, amma maharan suka bude wuta suka kashe mutum daya tare da jikkata wasu da dama.

Asali: Twitter
Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?
A kauyen Agbami, maharan sun yi wa mutane duka, amma ba a samu rahoton mutuwa ba a can, kamar yadda Punch ta rahoto.
Da aka tuntube shi, Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta Jihar Benue, DSP Udeme Edet, ya ce an tura jami’an tsaro zuwa yankunan da abin ya shafa a Makurdi.
Kakakin ƴan sandan ya kuma ba da hakuri tare da tabbacin cewa rundunar za ta fitar da ƙarin bayani nan ba da jimawa ba.
Hafsan soji ya koma Benue da zama
A wani labarin, kun ji cewa hafsan rundunar sojin kasa ta Najeriya, Laftanar Janar Oluyede, ya tattara ya koma Makurdi domin kawo ƙarshen haren ‘yan ta'adda a Benuwai.
Olufemi ya ɗauki wannan matakin sakamakon karuwar hare-haren makiyaya da ‘yan bindiga da suka yi silar mutuwar daruruwan mutane.
Hafsan Sojin zai gudanar da rangadi da kuma tsara yadda za a dakile hare-haren da gwamnatin jihar Benuwai ta ce ana kai wa jama'a kusan kullum.
Asali: Legit.ng