"Shi zai gyara Najeriya": An Roki Tsohon Shugaban Kasa Ya Dawo Ya Yi Takara a 2027
- Shugaban NRMO, Dr. Jibril Mustapha, ya bukaci Goodluck Jonathan da ya tsaya takarar shugaban kasa a 2027 don hada kan Najeriya
- Dr. Jibril Mustapha ya ce Najeriya na bukatar shugaban da zai magance matsin tattalin arziki, rashin tsaro, rashin aikin yi da ta’addanci
- Idan ba a manta ba, wata babbar kotun tarayya a Bayelsa, a 2022, ta yanke hukuncin cewa Jonathan zai iya sake yin takarar shugaban kasa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Shugaban kungiyar NRMO kuma dan a mutun Muhammadu Buhari, Dr. Jibril Mustapha, ya bukaci Goodluck Jonathan da ya tsaya takarar shugaban kasa a 2027.
Dr. Jibril ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Legas, yana mai cewa lokaci ya yi da Jonathan zai saurari kiran jama'a.

Asali: Getty Images
An roki Jonathan ya fito takara a 2027
Sanarwar da jaridar Punch ta gani, ta rahoto Dr. Jibrin yana cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Yayin da ake tunkarar zaben 2027, muna kira ga Jonathan da ya tsaya takara domin hada kan Najeriya da jagorantar ta zuwa tudun mun-tsira."
Dr. Jibril ya bayyana cewa Najeriya na fuskantar kalubale da dama, ciki har da matsin tattalin arziki, rashin tsaro, rashin aikin yi da kuma ta'addanci.
A cewarsa, ana bukatar shugaban da ke da gaskiya, nagarta, da kishin hadin kan kasa, domin fitar da Najeriya daga matsalolin da take fuskanta.
"Najeriya ta zo matakin da ake bukatar shugaban da zai hada kan al’umma ba tare da la’akari da kabila ko addini ba," inji Dr. Jibril.
Kungiya ta fadi dalilin kiran Jonathan
Shugaban kungiyar NRMO ya ce lokacin mulkin Jonathan an ga yadda ya mutunta dimokuradiyya tare da fifita jin dadin jama'a fiye da komai.
Dr. Jibril ya kara da cewa kungiyarsu na ganin Jonathan yana da hangen nesa da kwarewar da ake bukata wajen jagorantar Najeriya zuwa tudun-mun-tsira.
"Ina ganin turbar shugabancin Jonathan na hadin kai da ci gaban tattalin arziki shine abinda Najeriya ke bukata yanzu," inji dan a mutun Buhari.

Asali: UGC
Kungiyar Buhari da marawa Jonathan baya
Ya ce idan Jonathan ya karbi kasa, Najeriya za ta iya dawo da martabarta a idon duniya da kuma a cikin gida.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya rawaito cewa BYO kungiyar matasa ce da ke marawa tsohon Shugaba Muhammadu Buhari baya.
Jonathan dai ya gaza komawa kan mulki ne a 2015 lokacin da ya sha kaye a hannun Buhari a zaben shugaban kasa.
A zantawar Legit Hausa da matashin dan siyasa daga jihar Katsina, Kwamared Ubale Adamu, ya shaida cewa kuskure ne sake zabar Jonathan matsayin shugaban kasa.
An soki wannan kira da aka yi wa Jonathan
Kwamared Ubale ya ce matsalolin da ake cewa gwamnatin APC na fama da su, sun fi muni a lokacin gwamnatin Jonathan, musamman ma tsaro.
"Kar fa a manta, a lokacin sa ne 'yan Najeriya suka shiga tsoro marar misali, ko tashar mota, ko kasuwa ana tsoron zuwa, saboda fargabar za a sanya bam.
"Muna ji muna ganin aka rika sanya bam a masallatai, garuruwa da sauran wuraren tarukan jama'a. Kowa ya shaida, babu zama lafiya a mulkinsa."
Dan siyasar ya ce matsalar tattalin arziki ba iya Najeriya abin ya shafa ba, "ko a kasashen duniya, ana fama da matsalar tattali, kuma manufofin gwamnatin Tinubu na saukaka lamarin."
"Jonathan na da 'yancin sake yin takara" - Kotu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wata kotun tarayya da ke Bayelsa ta ce har yanzu Jonathan yana da ikon sake tsayawa takara duk da karbar rantsuwa sau biyu.
A hukuncin da ya yanke a 2022, Mai shari'a Hamma Dashen, ya bayyana cewa babu wata doka da za ta hana Jonathan sake tsayawa takarar shugaban kasa.
A cewarsa, marigayi shugaban kasa Umaru Musa Yar'Adua ne ya lashe zabe a 2007 ba Jonathan ba, kuma ba a gudanar da zabe a 2010 ba, don haka Jonathan bai saba doka ba.
Asali: Legit.ng