"Akwai Gagarumar Matsala," Jonathan Ya Yi Magana kan 'Shirin' da Ake Zargin APC Ta Kinkimo

"Akwai Gagarumar Matsala," Jonathan Ya Yi Magana kan 'Shirin' da Ake Zargin APC Ta Kinkimo

  • Goodluck Jonathan ya hango haɗarin da ke tunkaro Najeriya matuƙar ƴan siyasa suka mayar da ƙasar mai mulkin jam'iyya ɗaya
  • Tsohon shugaban kasar ya ce maida Najeriya ƙasa da jam'iyya ɗaya ke riƙe da mulki don cika burin wasu ƴan siyasa ba alheri ba ne
  • Ya ce idan akwai bukatar sauya tsarin siyasa, to ya zama dole a gayyato ƙwararru da masana domin tsara komai yadda ya dace

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya yi gargaɗin cewa yana da matuƙar haɗari ga Najeriya ta rikide zuwa ƙasar da jam’iyya ɗaya ke mulki.

Jonathan ya ce ba zai zama alheri ga Najeriya ba ta koma ƙasa da jam'iyya ɗaya ke kan mulki matuƙar ba a zauna da kwararru sun tsara yadda za a tafiyar da al'amura ba.

Goodluck Jonathan.
Jonathan ya ce Najeriya na iya faɗawa rikici idan aka maida ƙasar tsarin jam'iyya ɗaya Hoto: Goodluck Jonathan
Asali: Getty Images

Ya faɗi haka ne a Abuja a taron bankwana da tsohon dattijon ƙasa, Edwin Clark, ɗan siyasa kuma jagoran kabilar Ijaw, wanda ya rasu a watan Fabrairu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace matsala Goodluck Jonathan ya hango?

Jonathan ya ce duk wani yunƙuri na juyar da tsarin siyasar Najeriya zuwa na jam’iyya ɗaya ta hanyar dabaru don cika burin wasu ‘yan siyasa na kashin kai, na iya jefa ƙasar cikin rikici.

Tsohon shugaban ƙasar ya ce:

“Idan har dole ne Najeriya ta koma tsarin jam’iyya ɗaya, to sai an tsara shi da kyau, a sa kwararru su tsara shi, kuma sai an fahimci menene tsarin da ake son shiga.
“Amma idan aka zo da hakan ta bayan gida ta hanyar dabarun da maguɗin siyasa, to mu sani muna tunkarar rikici ne.”

Ana zargin APC da shirin canza tsarin siyasa

Gargaɗin Jonathan ya biyo bayan zargin da wasu ‘yan Najeriya ke yi cewa ƙasar na dab da rikidewa zuwa jam’iyya ɗaya, duba da yawan sauya sheƙar da ake yi daga jam’iyyun adawa zuwa APC mai mulki.

Ana zargin wasu gwamnoni PDP irin su Umo Eno na Akwa Ibom da Ademola Adeleke na Osun, suna mara wa burin tazarcen Shugaba Tinubu baya, lamarin da ke ƙara raunana jam’iyyun adawa.

Jonathan ya ce wasu ƙasashe sun samu nasara da tsarin jam’iyya ɗaya ne saboda tarihi da al’adunsu, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Jonathan.
Goodluck Jonathan ya ba da mafita kan yunkurin maida Najeriya tsarin jam'iyya ɗaya Hoto: Goodluck Jonathan
Asali: Getty Images

Hatsarin tsarin jam'iyya ɗaya a Najeriya

Amma a cewarsa, Najeriya na da tarin bambance-bambance na kabila, addini da siyasa, wanda ke bukatar tsarin da ya dace na gaskiya da adalci.

“A wasu ƙasashe, jam’iyya ɗaya ta taimaka. Julius Nyerere ya yi amfani da tsarin a Tanzaniya don kwantar da tarzoma bayan samun ‘yancin kai.
"Ya fahimci cewa yawan kabila da addinai na iya kawo rabuwar kai. Amma ya tsara hakan ne da niyya mai kyau, ba wai ta bayan gida ba."

- Goodluck Jonathan.

Yadda 'yan Najeriya ke kallon Jonathan

Goodluck Jonathan tsohon shugaban ƙasa ne da yawancin 'yan Najeriya ke ganin ya yi mulki cikin natsuwa da kwanciyar hankali.

Kodayake akwai sukar salon mulkinsa kan rikicin Boko Haram da yadda ake gudanar da tattalin arziki da yaki da cin hanci.

A mulkinsa daga 2010 zuwa 2015, Jonathan ya kafa tarihin zama shugaban ƙasa na farko da ya miƙa mulki cikin salama bayan faduwa zaɓe, wanda hakan ya jawo girmamawa daga ƙasashen duniya.

A yau, yana da matsayin dattijo da ke bada shawara mai amfani kan zaman lafiya da dimokuraɗiyya.

Gargadinsa game da hatsarin da ke tattare da ƙasar da jam’iyya ɗaya ke mulki ya ƙara fito da shi a matsayin mai kishin ƙasa.

Shawarwarinsa kan bukatar tafiyar da tsarin siyasa da adalci da shawarwarin masana na nuna damuwarsa game da makomar Najeriya.

Kalamansa kan hadarin gurgunta jam’iyyun adawa na da tasiri a cikin siyasa da ra’ayin jama’a.

PDP na shirin tsayar da Jonathan takara?

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta musanta raɗe-raɗin cewa tana shirin sake dawo da Goodluck Jonathan ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027.

Rahotanni sun nuna cewa wasu ƴan siyasa a Arewacin Najeriya na son Jonathan ya fito takara, saboda a ganinsu zai iya tsamo ƙasar da halin ƙaƙanikayi.

Sai dai ofishin muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Ambasada Umar Damagum ya ce ko kaɗan babu shirin dawo da Jonathan domin alamu sun nuna ya jingine siyasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262