'Tabbas Na Yi Kuskure': Bello El Rufai Ya Nemi Afuwar Goodluck Jonathan

'Tabbas Na Yi Kuskure': Bello El Rufai Ya Nemi Afuwar Goodluck Jonathan

  • Dan majalisar wakilai a jihar Kaduna, Bello El-Rufai, ya nemi afuwar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan
  • El-Rufai ya nemi afuwar ne bayan sukar tsohon shugaban kasar inda ya ce rashin wayonsa ne ya sa ya soke shi
  • Ya bayyana cewa sai bayan ya ga mahaifinsa na shirin ziyartar Jonathan domin shawarwari ne ya gane irin mulkin kirki da ake da shi a wancan lokaci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Ɗan majalisar wakilai, Bello El-Rufai, ya yi magana kan salon mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

El-Rufai ya ce rashin wayonsa ne da rashin sani ya sa ya soki tsohon shugaban kasar a wancan lokaci.

Bello El-Rufai ya nemi afuwar Jonathan
Bello El-Rufai yi nadamar sukar Goodluck Jonathan. Hoto: Bello El-Rufai.
Asali: Twitter

Bello El-Rufai ya yi nadamar sukar Jonathan

Da yake magana a shirin 'Politics Today' na Channels TV, dan majalisar ya nemi afuwa bisa yadda ya soki mulkin Jonathan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jonathan ya rike shugaban kasa a Najeriya daga shekara ta 2010 zuwa 2015 kafin ya mika mulki bayan faduwa zabe.

Dan majalisar daga jihar Kaduna ya ce rashin wayonsa ne ya hana shi fahimtar cewa an samu mulkin kirki a lokacin Jonathan.

A cewarsa, sai lokacin da ya ga mahaifinsa yana shirin ziyartar Jonathan domin shawarwari ne ya gane gaskiyar al’amura.

Bello ya ce:

“Lokaci guda na kai ziyara wurin mahaifina, na ga yana shirin fita, na tambaya inda zai je.
"Sai ya ce min zai je ya gana da shugaban kasa Jonathan. Na tsaya, domin ni a lokacin ban waye ba, ina yawan sukarsa.
“A lokacin, ban gane cewa muna da mulki ba. Yawancin matasa suna haka, saboda rashin fahimta ko girman kai.
Bello El-Rufai ya bayyana nadamar da ya taba yi
Bello El-Rufai ya nemi afuwar Goodluck Jonathan. Hoto: Bello El-Rufai.
Asali: Twitter

Abin da ya taba zuciyar Bello El-Rufai

Bello El-Rufai ya ce lokacin da ya samu labarin mahaifinsa zai ziyarci Jonathan, jikinsa ta yi sanyi inda ya bukace shi da ya nema masa afuwa.

Ya yaba masa kan dattakun da ya nuna musamman lokacin da ya fadi zaɓe a shekarar 2015 da aka gudanar tsakaninsa da Muhammadu Buhari.

Ya kara da cewa:

“Na ji mahaifina na cewa zai tuntubi Jonathan. Sai na ce masa: ‘Don Allah, idan ka hadu da shi, gaya masa na tuba.
"Yanzu na waye, na ce matsalar tana cikin tsarin da ake da shi yanzu saboda matsalar shugabanci da ake yi.
"Na ambaci Jonathan ne saboda yana da wahala mutum ya fadi zabe a Afrika ya sauka, ya yi hakan.”

Bello ya magantu kan rigimar El-Rufai, Uba Sani

Kun ji cewa Hon. Bello El-Rufa'i ya ce ba ya jin daɗin rikicin da ke faruwa tsakanin mahaifinsa, Nasir El-Rufa'i, da gwamna Uba Sani.

Bello ya bayyana cewa ba ya tsammanin suna rigima da juna, domin ba wanda ya fito ya zagi daya a gaban shi ko ya bayyana wata gaba.

Dan majalisar ya ce bincike ba laifi ba ne, amma idan ana yin sa domin tozarta wani ko zalunci, Allah ne kawai zai hukunta mai aikata hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.