Zaben 2027: Kusoshin PDP Suna So a Kyale Arewa, a Dauko Dan Takara daga Kudu
- Wasu jiga-jigan PDP da ke karkashin "Concerned PDP Stakeholders" sun bukaci a bai wa Kudu damar tsayar da dan takara a 2027
- Sun danganta rikicin jam’iyyar da rashin bin doka da kundin tsarin mulki, tare da jaddada sahihancin mukamin Sam Anyanwu na Sakatare
- Kusoshin sun gargadi PDP da ta gaggauta bin doka tare da aikawa INEC da manufar taron NEC domin ceto jam’iyyar daga durkushewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wasu manyan jiga-jigan PDP da suka haɗu a ƙarƙashin "Concerned PDP Stakeholders" sun buƙaci jam’iyyar ta tsayar da dan takara na shugaban kasa na 2027 daga Kudu.
Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ne ya karanta sanarwar bayan taron da suka gudanar a birnin Abuja a ranar Litinin.

Asali: Twitter
Abubuwan da za su iya jawo rushewar PDP
Jiga-jigan sun ce PDP na cikin rikici ne saboda wasu mutane sun ƙi bin kundin tsarin mulkin jam’iyyar, kamar yadda Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun danganta matsalolin da PDP ke ciki da sabanin da aka samu na wani sashe na kundin tsarin mulki da kuma hukuncin kotun koli game da kujerar babban sakataren jam’iyyar.
Sun nuna damuwa cewa idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, jam’iyyar za ta iya rushewa sakamakon rikicin cikin gida, son zuciya, da rashin bin doka, irin waɗanda suka jawo mata rashin nasara a zaben 2023.
Kusoshi sun nemi a kai tikitin PDP Kudu
A matsayin mafita, sun nemi PDP ta bayyana a hukumance cewa dan takararta na shugaban kasa a 2027 zai fito daga Kudu.
Sun kuma sake tabbatar da Sanata Sam Anyanwu a matsayin sahihin Sakatare Janar na jam’iyyar, bisa hukuncin kotun koli.
Ƙungiyar ta bayyana cewa bisa tsarin jam’iyyar, babban sakatare ne kaɗai ke da ikon fitar da sanarwar taro a hukumance.
Sun ƙara da cewa ba za a iya cire Anyanwu daga muƙamin ba sai a taron gangamin jam’iyya da aka shirya yadda ya kamata, domin yana cikin mambobin kwamitin zartaswa na kasa.

Asali: Twitter
Kusoshi sun fadawa PDP mafita gabanin 2027
Sanarwar da Wike ya karanta ta bayyana cewa:
“A cikin adalci, haɗin kai da bin tsarin rabon mukamai na ƙasa, da girmama tsarin mulkinmu, ya kamata PDP ta tsayar da dan takararta na 2027 daga Kudu.”
A ƙarshe, sun nemi shugaban jam’iyya da babban sakatare da su haɗa hannu wajen aika wa INEC da takardar sanarwar taron NEC.
A cikin sanarwar, su fadawa INEC manufar taron, wanda suka ce hakan ne kadai halastaccen matakin da zai sa jam'iyyar ta ci gaba da tafiya bisa doka.
Manyan kusoshin PDP sun koma APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jam'iyyar adawa ta PDP ta gamu da babbar matsala a jihar Legas yayin da wasu jiga-jiganta suka sauya sheka.
Mai magana da yawun jam'iyyar tare da wasu manyan shugabanninta sun fice daga cikinta APC mai mulki a jihar da ma kasa baki daya.
Wadanda suka sauya shekar, sun bayyana cewa matakin da suka ɗauka ya yi daidai domin jam'iyyar PDP ta riga da ta mutu murus a jihar.
Asali: Legit.ng