'Yan Bindiga Sun Cinnawa Gidajen Mutane Wuta a Kwara, An Hallaka Mutum 1

'Yan Bindiga Sun Cinnawa Gidajen Mutane Wuta a Kwara, An Hallaka Mutum 1

  • Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan ƙungiyar Mahmuda ne sun kai hari a Kwara, inda suka kashe mutum ɗaya, da ƙone gidaje
  • Maharan sun kai harin daga ƙarfe 6:00 kuma an ce sun ci karen su ba babbaka na tsawon awanni sakamakon rashin 'yan sa kai a garin
  • Daga bisani ne aka ce sojoji da ‘yan sa kai daga wasu garuruwa suka fatattaki maharan, yayin da 'yan sanda ke gudanar da bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara - Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan ƙungiyar ‘Mahmuda’ ne, sun kai hari garin Karongi da ke ƙaramar hukumar Baruten, jihar Kwara, a ranar Lahadi.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kashe mutum ɗaya, tare da kona gidaje da dama, inda suka ci karensu ba babbaka sakamakon rashin 'yan banga a yankin.

'Yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar Mahmuda ne sun kashe mutum 1, sun kona gidaje a Kwara
Taswirar Najeriya da ke nuna jihar Kwara. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

'Yan bindiga sun farmaki kauyen Kwara

Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun mamaye garin tun daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa 11:00 na safe, kafin dakaru da 'yan sa kai su fatattake su, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da cewa rundunar ‘yan sanda ta ce ba ta da masaniya kan harin, rundunar sojin Najeriya da sarkin masarautar Yashikira, Alhaji Umoru Sariki, sun tabbatar da faruwar lamarin.

Sarkin Yashikira ya tabbatar da cewa:

“Eh, maharan daga ƙungiyar Mahmuda sun kai hari a Karongi da misalin ƙarfe 6:00 na safe. Sun kashe mutum ɗaya kuma sun kona gidaje da dama.”

Sarkin Yashikira ya fadi yadda harin ya faru

Ya ce sun shafe tsawon sa’o’i biyar suna harbe-harbe, sakamakon rashin 'yan sa kai da suka tafi bukukuwan Sallah da kuma halartar taron horo.

Alhaji Umoru ya ƙara da cewa sai da suka je ƙauyukan da ke kusa domin tura 'yan sa kai, wadanda suka samu nasarar fatattakar maharan da misalin ƙarfe 11:00 na safe.

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kwara, Adetoun Ejire-Adeyemi, ta ce ba ta da masaniya game da harin.

Adetoun ta ce:

"Gaskiya ba ni da masaniya kan faruwar wannan lamari. Amma zan gudanar da bincike tare da fitar da cikakken bayani."
Rundunar sojin Najeriya da 'yan sa kai sun fatattaki 'yan bindigar da suka kai hari Kwara
Dakarun rundunar sojin Najeriya yayin da suke rangadi a dazuka. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Sojoji sun rahoto kone gidaje da mutuwar mutum

Sai dai Punch ta rahoto mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya ta 22 Brigade da ke Sobi, Ilorin, Laftanar Stephen Nwankwo, ya tabbatar da harin a ranar Litinin.

Ya ce:

“Kwarai, lamarin ya faru. Na samu rahoto. Ɗaya daga cikin 'yan sa kai ya rasa ransa, yayin da ‘yan bindigar suka ƙona wasu gidaje."

Ya ƙara da cewa:

“Sojoji sun samu kiran gaggawa, lamarin da ya sa suka nufi garin. Wanda aka kashe na daga cikin 'yan sa kai da suka yi wa sojojin rakiya zuwa kauyen.”

'Yan bindiga sun bude wuta a Kwara

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu ƴan bindiga dauke da makamai sun kai hari mai muni a jihar Kwara da ke Arewa ta Tsakiya, inda suka kashe mutane shida.

Harin ya auku ne a yankin Ilesha-Baruba, inda aka ce maharan suka bude wuta kan mai uwa da wabi, a wani hari na ba-zata da suka kai.

Rundunar ƴan sandan jihar Kwara ta tabbatar da faruwar lamarin, yayin da ta bayyana cewa an kama wani da ake zargi da ba wa maharan bayanai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.