Peter Obi Ya Ci Gyaran Tinubu, Ya Fadi Hanyar da zai bi wajen Cire Tallafin Man Fetur
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya caccaki manufofin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
- Peter Obi ya ce da shi ne, zai cire tallafin man fetur amma ta hanyar da ta dace kuma ba tare da jefa mutane cikin wahala ba
- Obi ya ce rashin tsari wajen aiwatar da manufofin da kuma fifita manyan ayyuka fiye da tsaro na jefa ƙasar nan a cikin haɗari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - 'Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, ya sake caccakar gwamnatin Bola Tinubu kan yadda take tafiyar da wasu daga cikin manyan manufofinta.
Peter Obi ya yi magana ne yayin da ake kokarin bikin ranar dimokuradiyya a ranar 12 ga watan Yuni na 2025.

Asali: Facebook
A wata hira da ya yi da Arise TV, Obi ya ce duk da yana goyon bayan cire tallafin man fetur, amma hanyar da aka bi wajen aiwatar da shi na cike da matsala.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Obi: 'Da ni ne, zan cire tallafi da tsari"
Peter Obi ya jaddada cewa cire tallafin fetur yana daga cikin kudurorinsa tun kafin zaɓen 2023, amma zai aiwatar da shi ne ta hanya mai tsafta da kare rayuwar al’umma.
Obi ya kara da cewa kafin a aiwatar da cire tallafi, ya kamata a fara da kawar da cin hanci, da bayyana yadda za a kashe kudin da aka samu, sannan a samar da tsarin da zai karbu ga kowa.
Obi ya soki karya darajar Naira da gina tituna
A bangaren karya darajar Naira, Obi ya ce hakan ba laifi ba ne, amma kamata ya yi a fara da bunkasa samar da kayayyaki a cikin gida kafin a dauki wannan mataki.
Obi ya ce:
“Babu laifi a karya darajar kudin kasa, amma sai idan kana da tattalin arziki mai inganci.
A halin yanzu, ba ma samar da komai. Ba mu da wani abin da zai ja hankalin masu zuba jari,”
Har ila yau, ya soki fifikon da gwamnati ke bai wa manyan ayyuka kamar ginin titin ruwan teku daga Legas zuwa Calabar fiye da batun tsaron ƙasa.
Daily Trust ta wallafa cewa Peter Obi ya ce:
“Shin wannan titi ya fi muhimmanci fiye da kare rayukan ‘yan Najeriya? Ni dai a shirye nake in yi duk abin da zai kare lafiyar al’umma,”
Obi ya kuma ce kwarewarsa a kasuwanci, gwamnati da harkokin mulki sun bambanta shi da sauran ‘yan takarar shugaban ƙasa da ke neman mulki.

Asali: Facebook
APC ta gargadi Ndume kan sukar Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta yi martani ga Sanata Ali Ndume kan sukar shugaba Bola Tinubu.
Sakataren yada labaran APC, Bala Ibrahim ne ya yi martani bayan Ndume ya kwatanta Tinubu da Goodluck Jonathan wajen faduwa zabe.
Bala Ibrahim ya ce APC na girmama Sanata Ali Ndume amma hakan ba ya nufin zai iya furta abubuwan da suka saba dokokin jam'iyya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng