Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani Game da Ginin Babbar Hanyar Legas Zuwa Kalaba
Aikin babbar hanyar Legas zuwa Kalaba wani babban yunƙuri ne na haɗa manyan biranen biyu da ke gabar tekun kudancin ƙasar domin kawo saukin zirga-zirgar mutane da kayayyaki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Wannan aikin zai sa yankin ya samun saukin alaka da sauran yankuna, zai tkuma aimaka wa harkokin kasuwanci da kuma sa zirga-zirga ta yi sauƙi, rahoton jaridar The Nation.
Hanyar za ta kasance babban titin kasuwanci, wanda zai hada Legas, birni mai yawan jama'a daga Yamma, zuwa Kalaba, birni mai tashar jiragen ruwa daga Gabas.
Kaddamar da wannan babban aikin zai samar da sabbin damarmaki ga al’umma da ‘yan kasuwa, wanda zai kawo babban canji ga tattalin arzikin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legas-Kalaba: Abubuwa 5 game da aikin
1. Tsayin titin
Gina babbar hanyar Legas zuwa Kalaba shi ne aikin samar da ababen more rayuwa mafi girma a Najeriya, wanda tsayin titin ya kai kilomita 700.
2. Kudin gina titin
Channels TV ya ruwaito gwamnatin tarayya ta ce za ta kashe kimanin Naira tiriliyan 15 domin gina titin, wanda zai kai ga Naira biliyan 4 a kowace kilomita 1.
3. Yadda za a gina titin
Aikin gina babbar hanyar zai gudana ne a cikin matakai, kuma ana sa ran za a kammala aikin a cikin shekaru takwas.
Za a fara da gina titin mai hannu biyu na tsawon kilomita 47.47 wanda zai dauki hanyoyin mota biyar a kowanne hannu, tare da titin jirgin kasa a tsakanin hannun biyu.
4. Garuruwan da titin zai bi
Babban aikin titin zai hada Legas da jihar Cross River, wanda kuma zai ratsa ta jihohi da dama da suka hada da Ogun, Ondo, Delta, Bayelsa, Ribas, da Akwa Ibom.
5. Manufar gina titin
Babban aikin gina babbar hanyar zai hada jihohi da dama a kan titi daya, da kawo haɓakar tattalin arziki a yankunan gabar tekun Najeriya.
Bugu da kari, ana sa ran hanyar za ta buɗe ƙarin filaye da wuraren shakatawa a bakin teku yayin da hakan zai rage cunkoso a Lekki, da kuma rage lokacin tafiya daga Legas zuwa Kalaba daga sa'o'i 12 zuwa sa'o'i 7.
Biyan haraji a titin Legas zuwa Kalaba
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito yadda 'yan Najeriya suka nuna adawa kan matakin gwamnati na cewa masu bin titin Legas-Kalaba da ake ginawa za su rika biyan ₦3000.
Gwamnati ta ce za a rinka biyan kudin ne matsayin haraji kullum idan titin ya kammala, lamarin da wasu ke ganin za a mayar da 'yan kasar saniyar tatsa.
Asali: Legit.ng