'Ndume ba Ya Iya Bakinsa,' Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Zazzafan Martani ga Sanatan Borno
- Kalaman Sanatan Borno ta Kudu, Mohammed Ali Ndume sun yamutsa hazo har ya jawo zazzafan martani daga fadar shugaban kasa
- Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa Sanata Ali Ndume yana yawan kalaman da bai san ma'anarsu ba
- Sanatan dai ya ce akwai wasu 'yan gata dake tafiyar da gwamnatin Bola Tinubu yadda suka ga dama, tare da gayawa shugaban karairayi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Fadar shugaban ƙasa ta caccaki Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Mohammed Ali Ndume, kan abin da ta kira barin zance a kafar yada labarai.
Sanata Ali Ndume ya yi zafafan maganganu a kan rashin tsaro da yadda ya ce wasu masu uwa a gindin murhu sun mamaye gwamnatin tare da gaya wa Shugaba Bola Tinubu karairayi.

Asali: Facebook
A martanin da ya wallafa a shafinsa na X, Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana cewa Sanata Ali Ndume ba shi da masaniya a kan maganganun da yake fada.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Onanuga: "Kalaman Ndume na karya ne"
Jaridar Vangaurd ta wallafa cewa Onanuga ya ce irin waɗannan kalamai da ba a tantance ba na sa Sanata Ndume, wanda tsohon shugaban masu rinjaye ne a majalisar dattawa, ya rasa mutunci a idon masu hankali.
A cewarsa:
“Ndume yana da 'yancin ya fadi ra’ayinsa, ko da kuwa ya zama dan adawa shi kaɗai a cikin jam’iyyar APC. Amma sau da yawa ya kan fadi abubuwa da ba su da tushe ko kuma ya gina hujjarsa a kan bayanai marasa ƙarfi, kamar yadda ya taɓa yi da labarin karya cewa an kai hari kan Janar Buratai."
Bayo Onanuga ya kalubalanci Ali Ndume
Mai magana da yawun shugaban ƙasa ya soki zargin da Sanata Ndume ya yi na cewa wasu shafaffu da mai ne ke mulki, yana mai cewa wannan Sanatan bai san ma'anar kalaman da ya fada ba.
Onanuga ya ce:
“Ya san ma’anar kalmar ‘kakistocrats’? Ko dai kawai yana jin daɗin amfani da kalmomin da ya gani suna burgewa ne?
“Wannan gwamnati na da hadimai masu kwarewa da gogewa, wasu ma fitattun kwararru ne kafin su shiga gwamnati. Yanzu haka suna aiki tukuru wajen gyara tattalin arzikin ƙasar nan don gina ginshiƙi mai ɗorewa.”

Asali: Twitter
Ya ce:
“Sakamakon ƙoƙarinsu ya fara bayyana. Tattalin arzikin Najeriya yana ƙara gyaruwa, kuma ana samun ci gaba mai ɗorewa.
Ndume ya ki marawa Tinubu baya
A wani labarin, mun wallafa cewa Sanata Ali Ndume, ya ce bai goyi bayan kudurin gwamnonin APC na sake tsayar da Shugaba Bola Tinubu a matsayin dan takarar jam’iyyar a zaben 2027 ba.
Ndume dake wakiltar Borno ta Kudu ya ce a halin da ake ciki a yanzu, musamman hauhawar farashin kayayyaki da matsalar tsaro, bai dace da yin irin wannan magana ba.
Ya kuma bayyana cewa ya fice daga taron da aka gudanar a fadar shugaban kasa lokacin da aka fara batun goyon bayan Tinubu, domin ya halarci zaman ne kawai don halartar taron koli.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng