"PDP ba Za Ta Ruguje ba": Sanata Ya Yi Bayanai kan Rikicin Jam'iyyar

"PDP ba Za Ta Ruguje ba": Sanata Ya Yi Bayanai kan Rikicin Jam'iyyar

  • Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Abba Moro, ya yi magana kan rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP
  • Sanata Abba Moro mai wakiltar Kudancin Benue ya bayyana cewa duk da rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar, ba za ta ruguje ba
  • Tsohon ministan cikin gidan ya kuma nuna ƙwarin gwiwar cewa Najeriya ba za ta koma ƙarƙashin jam'iyya ɗaya ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Abba Moro, ya bayyana cewa, akasin abin da ake yayatawa, jam’iyyar PDP ba za ta rushe ba.

Sanata Abba Moro ya kuma ba da tabbacin cewa Najeriya ba za ta zama ƙasa mai jam’iyya ɗaya ba.

Sanata Abba Moro
Abba Moro ya yi magana kan rikicin PDP Hoto: Senator Abba Moro
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta ce Abba Moro ya yi wannan bayani ne a garin Jos ranar Asabar, yayin babban zaɓen shugabannin PDP na yankin Arewa ta Tsakiya na jam’iyyar da aka gudanar a birnin Jos, babban birnin jihar Plateau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Sanata Abba Moro ya ce kan rikicin PDP?

Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa, bayan samun sababbin shugabanni, jam’iyyar PDP za ta farfaɗo daga halin da ta tsinci kanta a ciki, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

"Wannan taro ya yi nasara ƙwarai da gaske. Za ka iya ganin ƙwazo da himma, wakilai daga faɗin yankin Arewa ta Tsakiya, har da FCT, sun zo cikin farin ciki domin wannan zaɓe."
"Kamar yadda ku ka sani, wannan wani ɓangare ne daga cikin jerin matakan da PDP ke ɗauka domin magance rikicin cikin gida da ke damun jam’iyyar."
“Wannan tsarin yana kai wa ne zuwa babban taron ƙasa wanda za a gudanar da zaɓen sababbin shugabannin jam’iyya. Kada mu manta, rikicin da ake gani a jam’iyyar PDP ya samo asali ne daga rikicin shugabanci."
"Amma yanzu an fara zaɓen sababbin shugabanni daga matakin gunduma, zuwa ƙananan hukumomi, sannan zuwa jiha, har zuwa matakin yanki, sannan daga ƙarshe zuwa babban taron ƙasa, wannan tsari zai ba PDP sabuwar rayuwa.”

"PDP za ta ci gaba da ƙarfafa. Da irin yawan mahalarta taron nan da muka gani daga ko’ina cikin Arewa ta Tsakiya, da shugabanni irin su tsohon Gwamna Bukola Saraki da sauranmu da ke nan, zan iya tabbatar muku da cewa PDP ba za ta rushe ba, duk da jita-jitar da ake yadawa."
Abba Moro
Abba Moro ya ce Najeriya ba za ta koma karkashin jam'iyya 1 ba Hoto: Senator Abba Moro
Asali: Twitter
“Ba na jin tsoron Najeriya za ta koma ƙarƙashin jam’iyya ɗaya. Sam ba haka nake tsammani ba. Eh, sauya sheƙa na da tasiri, kuma yana iya haifar da firgici a farko."
"Amma bayan haka, mambobin PDP za su sake haɗuwa, su ƙuduri niyya, su mayar da kai wajen cigaban jam’iyya. Ina da yaƙini cewa PDP za ta dawo da ƙarfi fiye da wanda take da shi a baya."

- Sanata Abba Moro

Jigo a PDP ya buƙaci Peter Obi ya dawo jam'iyyar

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban jigo a jam'iyyar PDP, Segun Sowunmi, ya buƙaci Peter Obi ya dawo jam'iyyar.

Segun Sowunmi ya bayyana cewa lokaci ya yi da jam'iyyar PDP za ta yi zawarcin Peter Obi domin ya dawo cikinta.

Ya nuna cewa ya zama tilas jam'iyyar ta nemi tsohon gwamnan na jihar Anambra duba da irin goyon bayan da yake samu daga matasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng