LP: Ana Maganar Hadaka, Peter Obi Ya Fadi Jam'iyyar da zai Yi Takarar 2027
- Tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ya tabbatar da niyyarsa ta sake tsayawa takara a 2027 karkashin jam’iyyar LP
- Peter Obi ya ce akwai hannun gwamnatin tarayya a rikicin da ke cikin jam’iyyun adawa na LP da PDP a Najeriya
- Obi ya yi kira ga matasa da su kasance masu jajircewa domin tabbatar da cewa an kirga kuri’unsu a zabe mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi ya bayyana cewa zai sake tsayawa takara a 2027 karkashin jam’iyyar.
Obi ya bayyana haka ne yayin da yake amsa tambayoyi daga wasu matasa magoya bayansa cikin wani bidiyo da ke yawo a dandamalin WhatsApp na jam’iyyar a ranar Asabar.

Asali: Twitter
Vanguard ta wallafa cewa Obi ya ce rikicin da ke cikin jam’iyyun LP da PDP ba komai ba ne illa zagon kasa daga gwamnati mai ci don hana adawa yin tasiri a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Zan tsaya takara a LP' – Peter Obi
A cikin tambayar da aka yi masa kai tsaye kan wace jam’iyya zai yi amfani da ita wajen sake tsayawa takara a 2027, Obi ya ce:
“Zan ci gaba da tsayawa takara a jam’iyyar Labour. Ni ɗan jam’iyyar LP ne har yanzu.”
Yayin amsa wata tambaya daga wani matashi da ke nuna damuwa kan yadda ya ke nuna sakaci da rikicin LP, Obi ya ce,
“Rikicin da ke cikin LP da PDP gwamnati ce ke haddasa shi. Ku na iya fadan hakan a ko’ina.”
Obi ya bayyana abin da ya faru da shi a baya lokacin da marigayi shugaba Umaru Musa Yar’Adua ya sasanta rikicin jam’iyya tare da hada kai hukumar zabe a lokacin.
Peter Obi ya ce Umaru Musa Yar’Adua ya bukaci INEC ta warware rikicin jam'iyya a lokacin kuma nan take hakan ta faru.

Asali: Twitter
Bukatar gyara tsarin jam'iyyu a Najeriya
Obi ya ce idan ya samu damar shugabanci, zai tabbatar da cewa jam’iyyun siyasa sun yi aiki yadda ya kamata.
Ya ce:
“Wadanda ke cin gajiyar tsohon tsarin ba za su so canji ba. Amma dole ne mu dage domin canji mai amfani.”
Peter Obi ya yi maganar ajiye siyasa
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce kamata ya yi a saka iyakar shekaru ga ‘yan siyasa masu neman madafun iko.
Ya bayyana cewa zuwa lokacin zaben 2027 zai kasance yana da shekara 65, kuma baya son ya ci gaba da tsayawa takara bayan shiga shekaru 70.
A ƙarshe, ya shawarci matasa da su tabbatar da cewa an kirga kuri’unsu ta hanyar sanya ido da jajircewa.
Adewole ya nuna alamar hada kai da Obi
A wani rahoton, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar SDP a 2023, Adebayo Adewole ya nuna alamun janye takara wa Peter Obi a 2023.
Adebayo Adewole ya ce abin burgewa ne yadda Peter Obi ke tafiyar da harkokin siyasa ba tare da tashin hankali ba.
Baya ga haka, Adebayo Adewole ya ce suna tattauna yadda za su fatattaki Bola Tinubu a sirrance a zaben shugaban kasa na 2027.
Asali: Legit.ng