Duk da Gargaɗin Tinubu ga Masu Sauya Sheƙa, Ɗan Majalisa Ya Tattara Kayansa zuwa APC

Duk da Gargaɗin Tinubu ga Masu Sauya Sheƙa, Ɗan Majalisa Ya Tattara Kayansa zuwa APC

  • An sake samun wani dan majalisar tarayya da ya watsar da jamiyyarsa ta adawa zuwa APC mai mulki yayin da ake tururuwa cikinta
  • Hon. Ngozi Okolie ya sauya sheka daga LP zuwa APC a jihar Delta, yana mai cewa jam'iyyar ba ta da shugabanci mai kyau
  • Okolie ya ce ya yanke hukuncin ne bayan shawarwari da sarakuna da jama’ar mazabarsa, yana fatan wannan matakin zai kawo ci gaba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Asaba, Delta - Sauye-sauyen jamiyyun siyasa na kara karfi a jihar Delta kafin zaben 2027, yayin da wani dan majalisa ya koma APC.

Hon. Ngozi Okolie ya sanar da yin murabus daga jam'iyyar adawa ta LP tare da komawa APC mai mulki.

Dan majalisar tarayya ya koma APC
Dan majalisa daga Delta, Ngozi Okolie ya dawo APC. Hoto: Eugene Aligbe.
Asali: Facebook

'Dan majalisa ya fadi dalilin komawa APC

Dan majalisar wakilai mai wakiltar Aniocha/Oshimili ya sanar da ficewarsa daga LP a wani taron manema labarai da aka yi a Asaba, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Okolie ya ce a yanzu ba shi da wata alaƙa da LP inda ya barranta kansa da ita musamman duba da tsarin shugabancinta a yanzu.

Okolie ya nuna rashin jin dadinsa da yadda LP ke tafiya, yana mai cewa jam’iyyar ba ta shirya ba, kuma tana fama da rikice-rikice da dama.

Ya ce:

“Ba ni da wata alaka da jam’iyyar LP yanzu, ko da ban san gobe ba, na yanke wannan hukunci don ci gaban mutanena.”
“Ina....gaskiya, LP ba ta shirya ba, ba ta da shugabanci, matsaloli sun yi yawa. Ba za mu ci gaba a majalisa ba haka.”

- Cewar Hon. Okolie

Don majalisa ya watsawa jam'iyyarsa kasa a ido
Dan majalisar wakilai daga Delta, Ngozi Okolie ya.koma APC. Hoto: Legit.
Asali: Original

Matakan da ya bi kafin komawa APC

Hon. Ngozi Okolie ya bayyana cewa ya shiga APC ne tare da sauran masu son ci gaba, yana samun goyon bayan gwamna Oborevwori da sarakunan gargajiya.

Ya kara da cewa:

“Na yi shawarwari da sarakuna da mutanen yankina kan abin da nake nufin yi game da siyasa ta.
"Wasu sun yarda da ni, wasu ba su yarda ba, amma shugaba sai ya yanke hukunci.”

Ya ce bai so a dauka ya sauya sheka don bukatarsa ba, yana mai jaddada cewa yana so ya kawo ci gaba ga mazabarsa duba da halin da suke ciki a yanzu, Punch ta ruwaito.

“Ina da shekaru biyu a matsayin dan majalisa. Ina so in yi abubuwa nagari don mazabar Aniocha/Oshimili, ba kawai zama a jam’iyya marar nasara ba.”

- Cewar Hon. Okolie

Gwamnatin Tinubu ta gargadi masu sauya sheka

A baya, mun ba ku labarin cewa Gwamnatin Tarayya ta ce sauya sheka zuwa APC ba zai hana gurfanar da gwamnonin da ake zargi da cin hanci ba.

Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi shi ya yi wannan gargadi inda ya ce zargin haduwa da gwamnonin jihohin kafin sauya sheka karya ce tsagwaronta.

Hukumar EFCC ta yi magana kan haka, ta ce shugabanta ba shi da alaka da siyasa, kuma ba a yi wani taro da gwamna kafin sauya sheka zuwa APC ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.