An Taso Gwamna Dauda, an Faɗi Abin da Ya Sa Ya Kamata Matawalle Ya Dawo Mulki
- Wata kungiya a Zamfara ta bukaci Bello Matawalle ya sake tsayawa takara a 2027 saboda nasarorinsa wajen yaki da rashin tsaro
- Kungiyar ta ce Matawalle ya ba jami’an tsaro motoci 200, ya kaddamar da shirin 'Puff Adder' wanda ya kai ga ceto mutane da dabbobi
- Sun jaddada cewa gwamnatin yanzu ba ta tabuka komai ba duk da kashe kudi masu yawa, suna rokon Matawalle da ya dawo ya cika wa’adinsa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Wata kungiyar fararen hula a jihar Zamfara ta soki salon mulkin Gwamna Dauda Lawal.
Ƙungiyar 'Association of Zamfara North Concerned Citizens' ta bukaci tsohon gwamna Bello Matawalle da ya sake tsayawa takara a 2027.

Asali: Twitter
An yabawa ƙoƙarin Bello Matawalle a Zamfara
Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren kungiyar, Muhammed Usman Moriki, ya fitar a ranar Juma’a, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar ta yabawa da irin nasarorinsa wajen yaki da rashin tsaro da karfafa jami’an tsaro a lokacin mulkinsa.
Ta jaddada yadda Matawalle ya taka rawar gani tsakanin 2019 zuwa 2023 wajen fuskantar matsalolin tsaro na jihar duk da karancin kudi.
An kwatanta mulkin Matawalle da Gwamna Dauda
Kungiyar ta kwatanta mulkin Matawalle da na gwamna Dauda Lawal, tana cewa sabon gwamnan ya kasa kawo sauyi duk da karin kudaden shiga da yake samu.
A cewar sanarwar:
“Lokacin da yake gwamna, Dr Bello Matawalle ya samar da sababbin motocin aiki guda 200 ga jami’an tsaro tare da biyan kudadensu na aiki a kowane wata.
“Wannan ya faru ne cikin shekara biyu kacal, ba duka wa’adinsa ba, duk da kasafin kudi kadan idan aka kwatanta da na gwamnatin yanzu.”
Kungiyar ta lissafa wasu manyan ayyuka da ya aiwatar ciki har da kafa kwamitin tsaro, da tura ‘yan sanda 850 da kaddamar da 'Operation Puff Adder I da II' da jami’an Mopol 275.
A cewarsu, wadannan matakai ne suka kai ga ceto mutane 1,218 da aka sace, ciki har da ‘yan mata 279 na GGSS Jangebe, da kuma kwato dabbobi sama da 10,000.
Sun ce gwamnatin Bello Matawalle ta kuma kwato makamai masu yawa da suka hada da bindigogi AK-47 guda 154, rokoki da dubban harsasai.

Asali: Facebook
Ayyukan ci gaba na Matawalle a Zamfara
Kungiyar ta kuma ce aikin Ruga a Maradun ya kai kashi 90 cikin 100 kafin Matawalle ya kammala wa’adinsa a matsayin gwamna.
“Wadannan su ne shaidu na yadda ya fuskanci matsalar tsaro a cikin shekara biyu kacal.
"Ba ya zargin wanda ya gada, sai dai ya tunkari matsalolin da cikakken sanin mulki.”
- Cewar Moriki
Kungiyar ta zargi gwamnatin yanzu da gazawa wajen warware matsalolin tsaro da tattalin arziki.
Ta kira Matawalle, wanda yanzu Ministan Tsaron Najeriya ne, da ya dawo ya kammala wa’adinsa a matsayin gwamna.
An bukaci Dauda Lawal ya yi murabus
Mun ba ku labarin cewa wata kungiya a Arewacin Najeriya ta buƙaci Gwamna Dauda Lawal ya yi murabus saboda gazawa.
Kungiyar COGGAN ta ce gwamnan ya gaza musamman a bangaren tsaro inda ya kasa cika alkawuran da ya dauka.
Ta bukaci gwamnan ya bayyana yadda yake kashe kuɗaɗen jihar, tana mai cewa jihar ta cancanci shugabanci nagari.
Asali: Legit.ng