"Alkawurran Kamfe," Mai Martaba Sarki Ya Kunno wa Gwamna Wuta a Taron Jama'a

"Alkawurran Kamfe," Mai Martaba Sarki Ya Kunno wa Gwamna Wuta a Taron Jama'a

  • Sarkin Shao da ke ƙaramar hukumar Moro a jihar Kwara ya buƙaci Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya cika alƙawurran da ya ɗauka
  • Oba Job Obalowu Atolagbe ya buƙaci mai girma gwamna ya karrama Marigayi Cif Wole Oke ta hanyar zuba ayyukan more rayuwa a Moro
  • Ohoro na Shao ya ce marigayin mutum ne mai ƙwazo, wanda ya yi wa al'umma hidimar da ba za a taɓa mantawa da ita ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kwara - Sarkin Shao na ƙaramar hukumar Moro a jihar Kwara, Oba Job Obalowu Atolagbe, ya bukaci Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya cika alkawuran da ya dauka a lokacin kamfe.

Oba Atolagbe ya kuma roki gwamnan da ya kawo ci gaba da ingantattun ayyukan more rayuwa a garin Shao don girmama marigayi tsohon ɗan Majalisar dokokin jihar, Wole Oke.

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq.
Sarki ya bukaci gwamnan Kwara ya cika alkawurran da ya dauka lokacin kamfe Hoto: @AARahman
Asali: Twitter

Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a taron godiya da aka gudanar domin karrama marigayi jigon APC, Cif Wole Oke, The Nation ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wole Oke: Abin da sarkin ya ce a taron jama'a

A cewar sarkin:

“Cif Wole Oke mutum ne mai hangen nesa. Ya kasance jigon da ke kalubalantar siyasar wariya da mulkin kama-karya. Shi kadai ke ba mutane fata da kwarin guiwa a wancan lokacin.
"Shi ne ya gabatar da kudirin kafa Asibitin Kwararru da ke Ilorin. Ita ma makarantar sakandare ta gwamnati da ke Shao duk aikinsa ne.
"Ya tsaya tsayin daka don ganin Shao ta samu wutar lantarki. Marigayin ya bai wa gwamnatin yanzu goyon baya 100 bisa 100 har numfashinsa na karshe.”

Sarki ya miƙa bukata ga gwamnan Kwara

Basaraken ya kara da cewa Cif Oke mutum ne mai tawali'u da sauƙin kai, wanda ya yi wa al'umma hidima, kamar yadda Punch ta rahoto.

“Ya kasance abin misalin wajen tawali’u da saukin kai. Ina bukatar gwamna ya kafa Gidauniyar Cif Wole Oke domin ci gaba da raya abubuwan alherin da ya bari.
"Bai kamata a bari jajircewar wannan gwarzo ta tafi a banza ba. Ina kira ga ’yan siyasa da su guji fitintinu da gaba," in ji sarkin.

Gwamna AbdulRazaq ya tuna rayuwar Cif Oke

A nasa bangaren, Gwamna AbdulRazaq, wanda ya samu wakilcin Mai Ba Shi Shawara na Musamman, Saadu Saalu, ya bayyana marigayi Wole Oke a matsayin “tushen fata”.

A cewarsa:

“Gwamna yana cikin bakin ciki da alhini bisa rasuwar wannan dattijo, wanda kowa ya sani cewa tamkar uba yake a wurin gwamna.
"Na tsawon rabin karni, marigayi mahaifinmu ya na da kyakkyawar alaka da gidan AbdulRazaq.
"Ya kasance abin koyi a addinin kiristanci, dan Najeriya nagari mara son zuciya, kuma jagoran al’umma wanda ya kafa tarihi wajen ci gaban jama’a da tallafawa mutane.”

Gwamna AbdulRazaq.
Gwamna AbdulRazaw ya ce mutanen Kwara ba za su manta da Wole Oke ba Hoto: @AARahman
Asali: Twitter

Ya kara da cewa:

“Gwamnati da mutanen jihar Kwara baki daya za su yi kewar marigayin. Ya rasu a daidai lokacin da ake bukatarsa fiye da ko yaushe. Addu’ar gwamna ita ce Allah ya taimaki iyalansa da duk wadanda ya bari.”

Sarkin Ilorin ya yi wa yan siyasa nasiha

A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Ilorin, Mai Martaba Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari ya karɓi bakuncin tawagar jam'iyyar SDP a fadarsa da ke jihar Kwara.

Basaraken ya bukaci ‘yan siyasar Najeriya da su kasance masu gaskiya da rikon amana, su daina yi wa jama’a ƙarya da yaudara.

Ya jaddada cewa wajibi ne ga duk wani ɗan siyasa ya san mutanen da yake son mulka kuma ya fahimci halin da suke ciki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262