APC Ta Kara Yunkurowa, Shirin Haɗakar Atiku, Obi da El Rufai Ya Gamu da Babban Cikas
- Jam'iyyar LP ta gamu da babban koma baya yayin da ɗaya daga cikin manyan jiga-jiganta a Filato ya sauya sheƙa zuwa APC
- Victor Lah ya jagoranci manyan kusoshi zuwa APC, yana mai cewa ya dawo gida saboda an warware matsalolin da suka kore shi a baya
- Sanata Lah na ɗaya daga cikin ƴan kwamitin yakin neman zaɓen Obi/Datti a zaɓen da ya gabata na farkon shekarar 2023
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Plateau - Wani jigo a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na LP a zaben 2023, Victor Lar, tare da magoya bayansa, sun koma jam’iyyar APC a Jihar Filato.
Sanata Lar wanda tsohon dan APC ne kafin ya sauya sheka zuwa LP a zaben da ya gabata, ya ce matsalolin da suka sa ya bar jam’iyyar a baya yanzu an warware su.

Asali: Facebook
Babban jigon siyasar ya ce wannan dinke baraka ne ya sa ya yanke shawarar dawowa cikin APC, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me yasa jiga-jigan suka bar LP zuwa APC?
Sanata Lar ya ce wannan mataki nasu na dawowa APC ba wai kawai shawara ce ta kashin kai ba, mataki ne da jama’a da dama suka yarda da shi.
Ya bayyana cewa abubuwan da Shugaba Bola Tinubu ke yi da nasarorin da ya samu kawo yanzu sun jawo hankalin ‘yan siyasa da dama zuwa jam’iyyar APC
A cewarsa, a yanzu ƴan Najeriya na goyon bayan gwamnatin Shugaba Tinubu fiye da yadda aka yi tsammani.
Sanata Lar ya koma APC ne tare da shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin jihar Filato, Hon. Nandang Bako, da shugabannin jam’iyyar LP daga Filato ta Kudu.
Ya ce dawowarsu APC ba don neman wani muƙami ba ne face don su kara wa jam’iyyar kima, yana mai cewa bisa ra'ayin kansu suka sauya sheƙa ba tare da wani sharaɗi ba.
APC ta ƙara ruguza ƴan adawarta a Filato
Da yake karbar su, shugaban jam’iyyar APC na jihar Filato, Rt. Hon. Rufus Bature, ya ce dawowar Sanata Lar da magoya bayansa wani babban tarihi ne a fagen siyasar jihar.
Ya bayyana cewa dawowar Lar zuwa jam'iyyar APC wata babbar alama ce da ke nuna shirin canza akalar siyasar jihar Filato ya kankama.

Asali: UGC
Ya kara da cewa nan ba da jimawa "guguwar sauya sheƙa" za ta turnuƙe jam'iyyun siyasa a Filato domin akwai manyan mutane da ke shirin shigowa APC.
Shugaban APC ya yabawa Sanata Lar da magoya bayansa bisa wannan mataki da suka dauka, tare da tabbatar musu da cewa za a ba su duka hakkoki da damarmaki kamar kowa.
Ɗan Majalisa ya koma APC a Enugu
A wani labarin, kun ji cewa dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Udi/Ezeagu daga jihar Enugu, Hon. Sunday Umeha ya sauya sheka daga LP zuwa APC.
Sunday Umeha, wanda aka zaɓa a karkashin LP, ya sanar da sauya shekar sa zuwa APC a wani taron gangami da aka shirya a Enugu.
Ya bayyana rikicin cikin gida da ke addabar LP a matakin jiha da ƙasa a matsayin daya daga cikin dalilan da suka sanya ya bar jam’iyyar zuwa APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng