Siyasar Rivers: APC Ta Ce Tana Maraba da Gwamna Simi Fubara daga PDP
- Shugaban APC na Jihar Ribas ya bayyana cewa jam’iyyar ta buɗe kofa don karɓar Gwamna Simi Fubara idan ya yanke shawarar barin PDP
- Emeka Beke ya ce matakin zai kawo amfani ga APC da gwamnatin jihar, musamman a fannin gudanar da ayyuka da samun ci gaba
- Kungiyar dattawan jihar ta bayyana cewa ba ta goyon bayan kowace jam’iyya, burinta kawai shi ne dawowar Gwamna Simi Fubara ofis
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Jam’iyyar APC reshen jihar Ribas ta bayyana shirinta na karɓar Gwamna Siminalayi Fubara cikin jam’iyyar idan ya yanke shawarar ficewa daga PDP.
Shugaban jam’iyyar da kotu ta dawo da shi kan mukaminsa, Emeka Beke, ne ya bayyana haka cikin wata hira da aka yi da shi a ranar Talata, inda ya ce hakan zai amfani jihar.

Asali: Facebook
Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa dattawan jihar sun ce ba ruwansu da jam'iyyar da Fubara ke ciki, burinsu kawai shi ne a dawo da shi ofis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da rade-radin cewa Fubara na iya sauya sheƙa zuwa APC a wani ɓangare na yarjejeniyar sulhu da ke gudana don kawo ƙarshen rikicin siyasa a jihar.
Jam'iyyar APC ta ce za ta karbi Simi Fubara
Shugaban ma’aikatan ofishin shugaban APC na Rivers, Chizi Enyi, ya ce babu wani dalili da zai hana APC karɓar gwamnan cikin jam’iyya idan ya yanke shawarar sauya sheka.
An ruwaitto cewa shugaban APC na jihar ya ce:
“Tabbas za mu karɓe shi. Muna da wani zaɓi ne? Idan ya shigo APC, hakan zai ba mu fa’ida mai girma a harkokin jihar,”
Ya ce sau da dama gwamnonin da ba su fito daga jam’iyyar da ke mulki a ƙasa ba na fuskantar matsaloli wajen samun kuɗin gudanarwa da kuma halartar muhimman tarukan gwamnati.
APC ta shirya aiki tare da gwamna Fubara?
Shugaban na APC ya kuma bayyana cewa idan gwamna Fubara ya koma jam’iyyar su, za su ba shi goyon baya da shawarwari domin inganta shugabancinsa da walwalar al’ummar jihar.
Emeka Beke ya ce:
“Mu a matsayarmu na jam’iyyar hamayya, muna da abubuwan da za mu iya ba da shawara a kai, amma mun ɓoye su saboda tsari. Idan ya shigo APC, za mu buɗe masa zukatanmu,”
Ya kuma jaddada cewa da zarar Fubara ya shiga jam’iyyar, zai zama shugaba a matakin jiha, kuma hakan zai baiwa APC damar taka rawa a shirye-shiryen ci gaba da ayyukan gwamnati.
Martanin dattawan Rivers kan lamarin
A wani ɓangare kuwa, Ƙungiyar Dattawan da Shugabannin Jihar Ribas ta ce ba ta da alaka da kowace jam’iyyar siyasa, inda ta jaddada burinta na ganin Fubara ya ci gaba da zama gwamna.
Wani mamba a ƙungiyar, kuma tsohon kakakin PANDEF, Anabs Sara-Igbe ne ya bayyana hakan cikin wata tattaunawa da manema labarai a ranar Talata.

Asali: Instagram
Ya ce ba su amince da ci gaba da riƙe madafun iko da tsohon hafsun sojan ruwa, Ibok-Ete Ibas ba, yana mai cewa hakan ya sabawa kundin tsarin mulki.
A game da yiwuwar Fubara ya koma APC a matsayin hanyar sulhu da tsohon ubangidansa kuma ministan Abuja, Nyesom Wike, Sara-Igbe ya ce hakan ba shi ne damuwar jama’ar jihar ba.
Rikicin Rivers: Gwamna Fubara ya gana da Wike
A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Simi Fubara na jihar Rivers ya gana da Nyesom Wike a birnin tarayya Abuja.
Wata majiya ta tabbatar da cewa Fubara ya gana da Wike ne bisa jagorancin manyan 'yan siyasa a Kudancin Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa ganawar na cikin kokarin da ake domin ganin an shawo kan rikin siyasa da ya addabi jihar Rivers.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng