2027: Illolin da Yawan Sauya Shekar 'Yan Siyasa Ke Yi ga Ingancin Zabe a Najeriya
- Sauya sheka tsakanin 'yan siyasa a Najeriya na ci gaba da zama ruwan dare, inda masana ke ganin hakan na raunana jam’iyyun adawa da dimokradiyya
- Ana ganin cewa sauya sheka na janyo rashin aminci a tsakanin jama’a da kawo rudani, musamman idan wakilai sun canza jam’iyya ba tare da dalili ba
- Hakan na iya haddasa rikice-rikicen siyasa, lalata kawance, da sauya alkibla a majalisa ko gwamnati, lamarin da ke tasiri ga tafiyar da doka
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
A Najeriya, sauya sheka ya zama ruwan dare, musamman a tsakanin 'yan adawa domin neman tsira da kujerunsu ko damar samun wata kujera.
Wasu masana na ganin hakan na rage kwanciyar hankali a tsarin siyasa da raunin jam’iyyun adawa.

Asali: Facebook
Matsalolin sauya sheka a siyasar Najeriya
Wasu masana harkokin siyasa sun bayyana cewa sauya sheka yana dagula lamuran siyasa da dukkan jamiyyun da abin ya shafa, cewar rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauya sheka a siyasa wato yadda 'yan siyasa ke canza jam'iyya na iya yin tasiri mai yawa a zabe da kashe burin kafa dimokradiyya mai dorewa.
Hakan na raunana jam’iyyun adawa da kuma hana jama’a yarda da wakilan da suka zaba dalilin rashin tabbas daga bangarensu.
A wasu lokuta, sauya sheka kan haifar da rashin daidaito a kawance da sauya alkiblar siyasa.
Tasirin hakan kan bambanta da yanayin da ake ciki, musamman idan wanda ya sauya sheka fitacce ne ko kuma sabo ne a siyasa.
Legit Hausa ta duba wasu illoli da sauya sheka ke yi musamman ga zabe a Najeriya.
Wasu daga cikinsu sun hada da:
1. Raunana jam’iyyun adawa:
Sauya sheka na iya karya karfin jam’iyyun adawa da kuma rage musu kwarjini musamman a idon yan kasa da jam'iyya mai mulki.
Idan manyan 'yan siyasa sun sauya sheka, hakan na iya karya gwiwar magoya bayan jam’iyyar adawa da sanya su fara shakkar shugabancin jam’iyyar.
Duba da halin da ake ciki yanzu a Najeriya, kusan za a ce jam'iyyun adawa sun yi rauni saboda jiga-jigansu da suka koma jam'iyyar APC.

Asali: UGC
2. Rashin aminci tsakanin 'yan siyasa da jama’a:
Yawan sauya sheka na haifar da rudani da rashin kwanciyar hankali ga masu kada kuri’a wanda hakan yakan sa su rasa aminci ga 'yan siyasa da tsarin siyasa gaba ɗaya.
Wasu kan ji cewa wakilansu ba su da gaskiya ko biyayya ga jam’iyyarsu ko jama’ar da suka zabe su.
3. Rashin daidaito a kawancen adawa:
Sauya sheka na iya haifar da tangarda a kawance da kungiyoyin siyasa, musamman idan ya shafi manyan mambobi.
Wannan na iya sauya gwamnati, manufofin ta da kuma janyo sabani da rikice-rikice na cikin gida.
Mafi yawan haɗaka da ake ƙoƙarin yi ya samo asali ne domin neman hanyoyin kifar da gwamnatin da ke mulki ko don ba da tsinana komai ba ko kuma kawai saboda neman kwace mulki ƙarfi da yaji.
4. Sauya alkiblar siyasar kasa:
Idan 'yan siyasa da yawa suka sauya sheka, hakan na iya sauya rinjayen siyasa a majalisa ko gwamnati da ke mulki.
Zai iya tasiri ga yadda ake gudanar da doka da oda da kuma damar da adawa ke da ita na yin katsalandan ga gwamnati musamman idan ta kauce hanya.
Tsohon minista ya yi maganar sauya-sheka
A wata hira da jaridar TheCable, tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung ya caccaki masu sauya sheka da shirin hadaka.
Dalung a cikin hirar da aka yi da shi a watan Afrilun 2025 ya ce talakawan Najeriya da ke shan azaba ne ke zabe ba masu hadaka ba.
Ya ce saboda haka ya zama wajibi a inganta rayuwar al'umma madadin dogaro da masu sauya sheka da nufin za su ba su nasara a zaben 2027 da ke tafe.

Asali: Getty Images
Ana zargin ana sauya-sheka saboda tsoron EFCC
A baya, kun ji cewa akwai wasu jerin yan siyasa a Najeriya da suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC daga jam'iyyunsu daban-daban.
Wasu na zargin yan siyasar sun koma APC mai mulki ne domin kare kansu daga binciken hukumar cin hanci da rashawa, EFCC.
A lokuta da dama, wannan sauya sheka ka iya zamewa ‘yan siyasa mafakar kaucewa tuhuma da bincike mai zurfi na hukumar ta EFCC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng