Babachir Lawal: "Mun Gano Dalilin Turuwar 'Yan Adawa zuwa APC"

Babachir Lawal: "Mun Gano Dalilin Turuwar 'Yan Adawa zuwa APC"

  • Tsohon Sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya bayyana cewa akwai 'yan siyasa iri biyu dake gilmawa a tsakanin jam'iyyu
  • Babachir ya yi magana a kan wasu masu sauya sheka zuwa APC, inda ya ce da yawansu ba su da kishin kasa ko akidar taimakon talaka
  • Game da batun zaben 2027, tsohon Sakataren gwamnatin ya ce ba sa fargabar komai, domin za su je rumfunan zabe, su kasa, su tsare

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal, ya yi zargin cewa yawancin ‘yan siyasa da ke sauya sheka zuwa APC na yin haka ne don neman na abinci.

Babachir Lawal ya bayyana cewa yawancin masu sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki ta APC na yin haka ne don rage yunwar cikinsu da kare kansu amma ba don bukatun al'umma ba.

Babachir
Babachir ya dira a kan yan siyasa Hoto: Osigwe Omo-Ikirodah/Salihu Tanko Yakasai
Asali: Facebook

A wata hira da ya yi da Arise News a ranar Laraba, Babachir ya raba ‘yan siyasa kashi biyu, wadanda yake ganin su ne ke gilmawa a jam'iyyun siyasar Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babachir Lawal ya caccaki wasu 'yan siyasa

A hirar, Babachir Lawal ya ce akwai wadanda ke siyasarsu da niyyar yi wa al’umma hidima da kuma ke siyasa domin tara dukiya da wadaka da kudin al'umma.

Ya ce:

“Ba kowane dan Najeriya ne zai iya jimrewa yunwa ba, haka kuma ba kowa ne zai iya rayuwa cikin talauci ba. Saboda haka yawancin wadannan ‘yan siyasa da ke komawa APC suna yin hakan ne domin kare cikinsu da rayuwarsu ta jin dadi da suka saba da ita, wacce suka samu ta hanyar wawashe kudin jama’a."

Babachir ya ce sauya shekar da ake gani a siyasar Najeriya, ba alama ce ta biyayya ko kishin kasa ba, illa kawai wata hanya ce ta tsira da kariya ga 'yan siyasa.

Babachir ya magantu kan siyasar gwamnoni

Tsohon Sakataren gwamnatin na Muhammadu Buhari ya kalubalanci tasirin wasu gwamnoni da manyan jam’iyyun siyasa a wajen tara kuri'a yayin zabukan kasar nan.

Babachir
Babachir Lawal ya caccaki yan siyasa Hoto: Hoto: Osigwe Omo-Ikirodah
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa zaman dan siyasa gwamno ko wani babba a jam'iyya ba ya nufin zai iya shawo kan talakawa a wajen zuba wa jam'iyyarsa kuri'a.

Babachir ya ambaci misalin jihohin Delta da Borno, inda ya ce duk da gwamnoni ne ko ‘yan takarar mataimakin shugaban kasa, ba su iya jawo mafi rinjayen kuri’ar jama’arsu ba.

Ya ce:

“Ba mu damu da sauya sheka ba. Wannan abu ne da zai ci gaba da faruwa. Amma a zaben 2027, za mu je akwatin zabe, kuma za mu ga sakamakon. Muna da tabbacin cewa ba wani abu ne mai tasiri ba.”

Hadakar adawa: Babachir ya fadi matsayar PDP

A wani labarinnnn, mun ruwaito cewa Injiniya Babachir David Lawal, ya ce jam’iyyar PDP ba za ta taka wani muhimmin rawa ba a shirin da ake yi na hada kawancen siyasa gabanin 2027.

Babachir ya ce a duk zaman da suka yi tare da wasu manyan ’yan adawa domin kafa sabuwar hadaka, babu inda aka taba amincewa da amfani da PDP, saboda matsalar da ke cikinta.

Duk da haka, ya ce tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yana taka rawa a kokarin hada kan ‘yan adawa, wanda ake sa ran zai yi nasara kwace mulki daga hannun Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.